Posts

Showing posts from June, 2014

Ramadan khareeeem

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. Allah kayi salati da aminci abisa zababben zababbu, Annabinmu Manzonmu kuma Shugabanmu Muhammadu, tare da iyalan gidansa Inuwar al'ummah, da Sahabbansa Jagororin gaskiya. Yau insha Allahu zamu Qarasa magana akan Falalar Azumi sannan muci gaba da bayani akan rabe-raben Azumin da kuma falalar watan Ramadhan. 4. Hadisi daga Sayyiduna Abu-Umamah Albahily (ra) yace: "Nazo wajen Manzon Allah (saww) nace masa: "Ka Umurceni da wani abinda zan aikata wanda zai shigar dani Aljannah". Sai yace min "NA HOREKA DA YIN AZUMI. DOMIN HAKIKA BASHI DA MAKAMANCI". Sai na sake dawowa wajensa karo na biyu (Na sake tambayarsa akan haka). Sai yace min "NA HOREKA DA YIN AZUMI". (Imamu Ahmad da Hakim da Nisa'iy ne suka ruwaitoshi). 5. Daga Sayyiduna Sahlu bn Sa'ad Assa'idy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa: "HAKIKA ALJANNAH TANA DA WATA QOFA WACCE AKE KIRA "RAYYAAN". IDAN RANAR ALQIYAMA TAYI, ZA'A CE "IN...

balaifi bane

KA BAMA WANDA YA HANAKA. KA ZIYARCI WANDA YA KAURACE MAKA. KA KYAUTATA MA WANDA YA MUNANA MAKA. KA GAISAR DA WANDA YA DENA KULAKA. KAYI NASIHA DA AFWA GA WANDA YAI MAKA LAIFI. KAYI BAIWA GA MAKIYANKA KAMAR MASOYANKA.. WADANNAN SUNE HALAYE NA GIRMA, HALAYEN MASOYINMU (SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM).

dalilin shan azumi

DALILAN SHAN AZUMI GUDA GOMA SHA BIYU, Sharia ta Amincewa masu larura, su sha azumi, wasu zasu Rama wasu, su ciyar wasu baza, su ramaba, kuma ba zasu ciyar ba, gasu : Na daya: mara lafiya, zai sha azumi, idan ya warke sai ya rama Na biyu: matafiyi, zai sha azumi saboda tafiya, sai ya Rama daga baya. Na uku: mace mai jinin al'ada zata sha azumi idan tayi tsarki, ta Rama Na hudu: mai jinin haihuwa, idan jini ya dauke sai ta rama Na biyar, mai ciki, wacce Taji tsoran, wani Abu zai sameta, ko dan cikin ta Na shida, mai shayarwa ,wacce, Taji tsoran cutuwa, gareta ko dan take, shayarwa. Na bakwai, Tsoho , ko tsohuwa, wadanda, tsufa ya hanasu, azumi, sai su ciyar, Na takwas,: mahaukaci, idan ya warke, sai ya Rama idan kuwa, babu waraka ya sauka akansa babu ramuwa babu ciyarwa Na tara: Yaro, azumi akan yaro ba wajibi bane, sai dan sabawa Na goma, mai farfadiya, idan farfadiya, tazowa mutum, yana azumi, bazai ramaba idan ya farfado Na sha daya,: mai ciwan kishirwa, wanda bazai iya azumi ba,...

HUKUCIN AMFANI DA ABIN DA YAKE HANA AL'ADA A LOKACIN AZUMI

HUKUCIN AMFANI DA ABIN DA YAKE HANA AL'ADA A LOKACIN AZUMI Tambaya : Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske . Amsa : To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, amma da sharuda guda biyu : 1. Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Al bakarah aya ta 195 2. Ya zama da iznin miji ne, idan hakan ya shafe shi, kamar idan tana iddar da ciyarwa ta wajaba akanshi, sai ta yi amfani da abin da zai hana ta haila don lokacin ya kara tsawo kuma don ta kara masa yawan ciyarwa, to anan bai halatta ta yi amfani da abin da zai hana haila ba saida izninsa, ko kuma idan ya zama maganin zai hana daukar ciki to dole saida iznin miji. Saidai duk da ce...

maye burinka cikin wata maialfarma

MEYE BURINKA/KI A WATAN AZUMI..............?????!!!! Hakika kowane dayanmu yana da Bukata ta musamman a wajen Allah. To Watan Ramadhan da kuma Azumin cikinsa ya bamu dama mai yawan gaske domin biyan Bukatar tamu. 1- Lokacin Buda Baki ana karbar Addu'ar Mai Azumi. 2-Lokacin yin Sahur ma ana Karbar Addu'ar Mai Azumi. 3- A cikin Sallah lokacin Sujjadah ana karbar Addu'a,ga kuma lokaci ne na yawaita Sallolin Nafila. 4-Lokacin da ka taimakawa Dan uwanka saboda Allah,shima lokacin karbar Addu'a ne. 5-Lokacin Sauka ko gama Karatin Qur'aani,shima lokacin Karbar Addu'a ne. Hakika ga wanda duk ya ribanci wan nan Watan,to cikin Taimakon Allah zai sami biyan Bukatunsa daga Allah Madaukakin Sarki. Muna godiya ga Allah,wallahi cikin ikon Allah dukkan Ramadhan,sai na sami kusan biyan bukatar da nasa a gaba. Allah ya karbi ibadun mu gaba daya,ya kuma kiyaye mu Azabar Wuta,ya sanya mu a Aljannah!!!

kofofin aljanna

"ALJANNAH TANA DA QOFOFI GUDA TAKWAS, ACIKINSU AKWAI WATA WACCE AKE KIRA 'AR- RAYYAN' - BABU MAI SHIGA CIKINTA SAI MASU AZUMI" Fatana Shine: Allah yasa dani daku, da iyayenmu da iyalanmu da masoyanmu da dukkan Muminai mu samu Shiga ta wannan Qofar!!!. Ina muku fatan Alkhairi da addu'ar Allah shi karba mana dukkan ayyukanmu baki daya. Ameeen.

darrussa

ZA MU IYA SAMUN NASARAR RAYUWA DAGA DARUSSAN AZUMI 01 Category: Sinadarin rayuwa Published on Friday, 27 June 2014 00:00 Written by Bashir Yahuza Malumfashi Hits: 51 A yayin da muke tsimayar zuwan watan ibadar azumi, za mu yi tambihi ne, mu ga yadda za mu iya amfani da darussan azumin, wajen inganta da bunkasa rayuwarmu ta yau da kullum, yadda za mu iya cin ma nasarar rayuwa da su. daya daga cikin darussan da azumi ke koyarwa shi ne hakuri, domin kuwa kamar yadda al’amarin yake, mutum zai yi hakurin jure wa yunwa tun daga asubahi har zuwa faduwar rana, na tsawon kwanaki 29 ko 30. Idan har mutum zai iya yin hakurin yunwa da kishirwa haka, ke nan zai iya hakuri da duk wata wahala ko damuwa da za ta same shi. Wannan yana nuna mana cewa, a al’amuran da muke fuskanta na rayuwa, muna da bukatar hakuri. Za mu kasance cikin hakuri wajen zama da abokan zamanmu, kamar makwabta, abokan aiki, iyali da sauransu, domin kuwa abu ne na hakika, za mu rika fuskantar al’amura marasa dadi, ko na bacin rai...

karya waiyazubillah

KARYA... بِسْمِ اللهِ الْرَّحْمَنِ الْرَّحِيمِ Allah Ta'a Ya ce: "Lallai tsinuwar Allah ta tabbata a bisa MAKARYATA", "Kuma Ya ce: "An tsine wa Makaryata" kuma Ya ce: "Lallai Allah ba ya shiryar da mai barna kuma Makaryaci. A cikin Bukhari ya zo daga ruwayar samurah dan jundub- a cikin Hadisin Annabi (S .A .W)ya ce: "sai muka tarar da wani yana tsaye a kansa da gatarin karfe, sai ya tsaga kansa da idonsa ta kowanne bangare, amma da zarar ya gama sai ya sake komawa yadda yake,Haka zai yi ta yi har zuwa ranar kiyama, sai na ce da su wane ne wannan? sai suka ce" "Wannan shu ne wanda yake fitowa daga gidansa kuma ya yi karyar da kowa sai ya samu labarinta". Manzon Allah (s a w) ya ce: "Mumini yana sabawa da kowacce 'Dabi'a amma ban da yaudara da 'Karya" (Imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi)... lallai wanann hadisin babban wa'azine garemu mu da muke yin FECEBOOK DA SAUREN SOCIAL NETWORK.... gurin yada magan...

gaskiya mai daci

GASKIYA MAI DACHI * ******************** Yawancin Mutane sun dauki Azumi amatsayin wani lokaci ne wanda ake wuni da yunwa.. Don haka akwai Bukatar gyara abinci sosai domin idan lokacin shan ruwa (buda-baki) yayi, Kaci da yawa sai ka Qoshi. Don haka zaka ga wasu Har time-table sukeyi na Kala-kalan abincin da zasu rika yi akullum. Yawancin mutane suna Mantawa da BABBAN ABINDA YAFI MUHIMMANCI shine ka samu Tsoron Allah. Ta hanyar wuni da yunwa, so ake ka tuna da cewa akwai fa wasu bayin Allah wadanda ko yaushe cikin kwanakin shekara ahaka suke wuni, ahaka suke kwana!!! Ida ka dandana irin halin da suke ciki, to kaga kenan zaka fi jin tausayinsu da kokarin taimaka musu akoda yaushe. Abu mafi muhimmanci shine kaji acikin zuciyarka cewa ibada kakeyi, ka taimaka ma Makobtanka da 'yan uwanka, kuma ka samu Tsoron Allah azuciyarka. Time table na Ibadar nafilfili da Karatun Alqur'ani yafi Muhimmanci fiye da Timetable na abincin da zaka rika ci. Da yawa wasu basu da wata riba acikin yin Az...

abun da basa karya azumi

ABUBUWAN SHA BIYAR NE BA SA KARYA AZUMI:- abisa ittifaqin malamai na da dana yan zu (1) Ci Ko Sha Bisa Kuskure (2) Allura Idan Bata Abinci Ne Ba. (3) Sanya Kwalli Ga Maza Da Mata. (4) Amai Idan Har Ba Kirkirarsa Akayi Ba. (5) Yin Mafarkin Saduwa Da Mace Da Rana. (6) Amfani Da Magogin Baki Na Zamani(Broshi) (7) Diga Magani a Ido (8) Fitar Da Maziyyi (9) Shekar Inhela Ga Masu Ciwon Asma. (10) Amfani Da Turare Ko Kayan Kwalliya Ga Mata. (11) Hadiyar Yawu (12) Jika Jiki Ko Nitsewa a Cikin Ruwa (13) Habo Ko Jin Rauni (14) Wankan Janaba Bayan Alfijir Ya Keto (15) Dandana Abinci Matukar Ba'a Hadiye Ba. ALLAH YA HORE MANA ABIN MASARUFIN DA ZAMU YI AMFANI DA SHI A LOKACIN AZUMIN NAN, YA SADA MU DA DUKKAN ALKHAIRAN DAKE CIKIN WATAN RAMADAN AMEEEN

sojojin

Akalla Sojojin kasar Siriya 10 ne a ka kashe yayin da kasar Isra’ela ta kai hari ta Sama a kasar Siriya inda ‘yan tawaye ke ci gaba da fada da Dakarun gwamnatin shugaba Bashar Al-assad Harin ya auku a kusa da kan iyakokin kasashen biyu a wani yanki da kasar Isra’ela ke rike da shi na Golan Heights, kamar yanda wata kungiya mai sa idanu kan al’amuran da ke wakana a kasar ta tabbatar. Makamai masu linzami tara Isra’ela ta harbawa sojin kasar Siriya ta hanyar amfani da wani Jirgin sama, inda suka lalata tankokin yaki biyu da makaman atilare biyu. http://hausa.leadership.ng/node/1701

buda baki

ADDU'A GAMAI AZUMI IDAN ZAIYI BUDA BAKI. ==================== ذهب الظمأوابتلت العروق. وثبت الأجران شاءالله ٠ ZAHABBAZ ZAMA'U WABTALLATIL URUQU WASABATAL AJRU INSHA ALLAH ☀fassara☀ kishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah yaso. Dan Allah kuyi Like da share dinsa saboda yan uwanku su amfana. Allah ya hadamu acikin ladan baki daya.

maanar azumi

MENENE MA'ANAR AZUMI? Ans: Ma'anarsa a shari'a shine kamewa daga dukkan abubuwan da suke 6ata azumi,kamar ci da sha da Jima'i da sauransu, daga ketowar Alfijir zuwa faduwar Rana da niyyar bautawa Allah. MENENE DALILIN WAJIBCIN AZUMI? Ans: Dalilin wajibcin azumi shine fadar Allah madaukakin sarki "Ya ku wadanda kukayi Imani an wajabta muku yin Azumi kamar yadda aka wajabta wa wadanda suka gaba ceku ko kunji tsoron Allah". Kwanakine Kididdigaggu. Kuma hadisi ya ingata daga Abu huraira RA. Manzon Allah s.a.w. Yace " kuyi Azumi idan kun ganshi"........ Wannan kuwa umurni ne. Ana Iya daukar azumin koda mutum dayane yaga wata domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi dan Umar R.A yace "mutane sun rigeni ganin jinjirin wata saina gayawa manzon Allah s.a.w sai yace" suyi azumi". Duba Abu Dauda 2340, Hakim da Ibn Hibban suka inganta shi: Hakim 423. Ibn Hibban 3438. Amma mafi yawan malamai sunce ganin mutum daya ga watan to lallaine yazamto Adali w...

tabayar azumi

FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN. TAMBAYA TA : MENENE I'ITIKAFI? AMSA: Ma'anar I'itikafi a larabce shine lazimtar wani abu, da tsare kai. Amma ma'anar a Shari'a shine, lazimtar masallaci ga mutunin da ya kebance kansa, a wata siffa kebantacciya da nufin ibada. I'itikafi ya tabbata a cikin littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) da kuma Ijma'in malamai. Sobada haka sai a himmatu da yinsa sosai da sosai. TAMBAYA TA : A INA AKE YIN I'ITIKAFI? AMSA: Anayin I'itikafi ne a cikin masallatai, amma ba'ayi a musalla ko a gida . Dalilinmu kuwa shine nassin Al-kur'ani ya tabbatar da haka acikin fadin sa Allah ta'ala cewa,"KUMA KADA KU KUSANCE SU (MATANKU) ALHALI KUNA I'ITIKAFI A MASALLATAI……50." Kuma Imamul Bukhari ya bude babi a cikin sahihinsa cewa: 'Anayin i'itikafi ne a Masallatai baki daya', sai ya kafa hujja da ayar da ta gabata. Hafiz Ibn Hajar ya fada acikin Fatahul Bari cewa: Mafi yawan malamai su...

tambaya

Mallam don Allah menene hukuncin wanda yayi mafarki da azumi ??? Tambaya ta 2. Menene hukuncin wacce take magana da mijinta ko kuma suka kalle juna bada niyyar sha'awa ba amma kuma sai sha'awar ta motsa har takai da fitar ruwa (maniyyi) ??? Allah ya saka da Alkhairi Mallam (Daga Firdausi Shuaib Gezawa). AMSA ----- AMEEN FIRDAUSI. DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. 1. Wanda yayi mafarki a watan azumi mace ko namiji azuminsa yananan koda kuwa yafitar da maniyyi domin an dauke alqalami akan mutumin da yake bacci harsai ya farka. AMSAR TAMBAYA TA 2. Zataci gaba da azuminta babu komai. Domin Jabir bin Zaid (R.A) yace: "Wanda ya kalli mace ya fitar da maniyyi yaci gaba da azuminsa babu komi a kansa. Wannan shine abinda Imam Shafi'I (Babban almajirin Imam Malik), da Imam Thauri da Auza'iy duk suka tafi akai sunce: Babu wani dalili da yazo cewar fitar da maniyyi kadai yana karya azumi ba tare da jima'I ba. Amma jima'I ko an fitar da maniyyi ko ba'a fitar ba y...

saurayi da budurwa

HIRA TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA ...SAURAYI: sannu ƴan mataBUDURWA: Kaima sannuSAURAYI: Kamar na sanki,.... Amma na manta inda na sanki, ko a A.B.U ne?BUDURWA: Ba mamaki. A chan nake karatu, ina 300 level ne. Kaifa?SAURAYI: ni ina A.B.U Kano ne, ina karanta Islamic engineeringkuma ina 900 level ne ni. Kuma ina kaiwa 1,500level, sai in karbi digirina in fara neman aikiBUDURWA: Woo! Kai lier!!!SAURAYI: Ina kika ga laya anan! Sarka ce fa a wuyan nawa ba laya ba!BUDURWA: Ok I want to go!SAURAYI: gaskiya bana 2go amma ina textbookBUDURWA: No, I mean I am going home!!!SAURAYI: Gaskiya bazan iya goya kiba, kinyi nauyiBUDURWA: Kai wai wace secondary kayi ne?SAURAYI: Primary election aka fara saka ni, sanna aka maida ni secondary electionSAURAYI: Daga nan sai na koma B.U.K Zaria, bayan na gama sai na dawo A.B.U KanoBUDURWA: Lallai ka hadu!!!

saurin fita da anyi sallama

INA MASU SAURIN TASHI DAGA AN IDAR DA SALLAH KAMAR ANA MINTSININSU? TO KU ZO MUJI ABIN DA MANZO (S.A.W) YA FADA. Yau Hadisinmu zai yi magane game da wadanda suke saurin tashi daga sallah da zarar anyi Sallama. Kuma abin haushi sai kaga ma wata kila idan ya tashi ba'abin da ya tsinana. Ko kaga yaje kan gada ya zauna, ko majalisa ko kuma kawai ya tsaya a wajen masallacin sbda bai san tarin ladan da ya bari ba. Daga Abu Huraira (R.A) yace, Manzon Allah (S.A.W) yace, "Sallar mutum a cikin jama'a ana rubanya ladanta a kan sallarsa a gidansa da kasuwarsa, da rubi 25, wannan kuwa sbe idan yayi alwala, ya kyautata a alwala, sannan ya fita zuwa Masallaci,ba abin da ya fito da shi sai Sallah. Babu wani taku da zai yi face sai an daga darajarsa da shi, kuma an kankare masa zunubai da shi, to, idan yayi sallah, MALA'IKUN ALLAH BA ZASU GUSHE BA SUNA YI MASA ADDU'A, MATUKAR DAI YANA WAJEN DA YAI SALLARSA, SUNA CEWA; 'YA ALLAH KA YI MASA RAHAMA, YA ALLAH KAYI MASA GAFARA, YA ...

adduar buda baki

{ADDU'A IDAN MAI AZUMI ZAI BUDA BAKI} Wannan addu'ace wadda akeyi idan za'a buda baki idan lokacin shan ruwa yayi gata da LARABCI DA BOKO KAMAR HAKA: ﺫﻫﺐ ﺍﻟﻈﻤﺄ ﻭﺍﺑﺘﻠﺖ ﺍﻟﻌﺮﻭﻕ ﻭﺛﺒﺖ ﺍﻟﻸﺟﺮ ﺇﻧﺸﺎﻉ ﺍﻟﻠﻪ . ZAHABAZ-ZAM-U WABTALLATIL-URU UQ,WADHABATAL-AJRU INSHAAL-LAH. GA FASSARARTA: Qishiruwa tatafi,an yayyafawa jijiyoyi ruwa,kuma lada yatabbata in Allah yaso. HADITH daga Abdullahi bin amr al-AS yace:manzon Allah {SAW} YACE:"MAI azumi yana da addu'a da ba'a mayar da'ita idan yazo bude baki". Wato ma'ana duk bunda karoka lokacin buda baki karbabene dafatar Allah yakarbi addu'o'in mu yakuma sanyamuna cikin bayinda za'a "yanta wannan wata mai albarka amin.

manzon allah yace

Manzon Allah S.A.W yace: "wanda duk yayi salati a gareni ko wacce Juma'a sau arba'in (40) Allah zai shafe zunubansa gaba daya" Manzon Allah S.A.W yace: "mafi kusancin mutane a gareni ranar alkiyama sune wanda suka fi yawaita salati a gareni." Manzon Allah S.A.W yace: " wanda duk ya manta da yin salati a gareni hakika ya kaucewa hanyar Aljanna." Manzon Allah S.A.W yace: "babu wata addua face akwai hijabi tsakaninta da sama har sai an yi salati a gareni, idan akayi salati a gareni sai wannan addua ta keta hijaban nan a dagata zuwa sama." ma'ana duk wata addua da bawa zaiyi bazata wuce sama ba har sai yayi salati ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa salam. Shi yasa yana da kyau idan zamu roki Allah akan bukatun mu, mu fara da salati in mu gama kuma mu rufe da salati. Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu dama duk kasashen musulman da suke cikin tashin hankali. Ameen

anga wata

Anga Wata a Qasar Turkiyya Da Sauran Kasashen Turai:- Rahotanni Daga Qasar Turkiyya, Belgium, Rasha, Italiya Da Sauran Kasashen Gabashin Turai Na Nuna Cewa Hukumomin Addinin Musulunci Na Kasashen Sun Sami Rahoton Ganin Watan Ramadana Kuma Sun Bayyana Gobe Asabar a Matsayin 1 Ga Ramadan 1435 AH. Hakannan Kuma Hukumomin Kasar Yemen Sun Bayyana Asabar a Matsayin 1 Ga Ramadan 1435.

brazil

Dan wasan Brazil Dani Albes ya ce ficewar kasar Spain a gasar cin kofin duniya tun a zagayen farko babban darasi ne ga kasashen da ke fafatawa a gasar. A cewar dan wasan na Barcelona samun nasara ba karamin kalubale ba ne. Spain ce ta lashe kofin duniya a kasar Afrika ta Kudu a 2010 kuma a bana tun a tashin farko ne aka yi waje da Spain bayan ta sha kashi a hannun Holland da Chile a rukuninsu na B. “Wannan abin kunya ne”, a cewar Albes tare da yin jaje ga abokan wasan shi na Spain a Barcelona. Wannan dai kamar kira ne Albes ya ke yi wa ‘Yan wasan Brazil don su dage musamman yadda Medico ta rike su babu ci kafin su hadu da Kamaru a ranar Litinin domin samun hurumin tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

aikin da mai azumi yakamata yayi

MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI DINGA YI (2) ??? Nafil-fili: Anaso mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman kiyamul laili Saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara tabbata a gareshi yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: "Duk wanda yatsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada; an gafarta masa zunubansa da suka gabata". Bukhari ne ya ruwaito shi(1). Haka kuma Manzon Allah (S.A.W) yace: Wanda yayi sallah dare tare da liman har yagama za'a rubuta masa ladan kiyamullaili. Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A) Targib Wattarhib wanda Albani yayiwa tahkiki lambar (1078). "Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana tsawaita karatu a sallar dare a watan Ramadhan fiye da sauran sallolin dare, yace: Manzon Allah (S.A.W) yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a daya, kuma baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikin ta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari. Kuma bai gama raka'a biyu b...

yaku

بسم الله الرحماني الرحيم ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻛُﺘِﺐَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢُ ﺍﻟﺼِّﻴَﺎﻡُ ﻛَﻤَﺎ ﻛُﺘِﺐَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦ ﻗَﺒْﻠِﻜُﻢْ ﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺘَّﻘُﻮﻥَ ¤ Ya ayyuhallatheena amanookutiba Alaykumu assiyamu kamakutiba ala allatheena min qablikum laAAallakumtattaqoon ¤ O you who have believed, decreed upon you is fasting as it was decreed upon those before you that you may become righteous ¤ Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa. 'sadaqallahul Azeem' - From the Al-Qur'an Khareem_2:183 Allahumma Ballighna Ramadan -

AIRTEL UNLIMITED BBM SUBSCRIBTION CODE AKAN ANDROID.

AIRTEL UNLIMITED BBM SUBSCRIBTION CODE AKAN ANDROID. Kuna Tare Da Nasir Wixard. Airtel Nigeria sun gabatar da sabon unlimited plan na BBM ga masu amfani wayar android da Iphone domin saukaka ma costomer nasu masu amfani da BBM akwan wayoyin android. Sanin kowane tuni wayoyin android sunbi takwarorin na Blackberry wajen amfani da BBM wato BlackBerry Messenger,kuma wannan sabon tsarin na airtel unlimited ne. _ Domin yin subscribing na monthly Airtel BBM plan akan android da wayoyin i OS ,danna 440 22# akan N300 kacal. _ Domin yin subscribinf na weekly airtel BBM plan akan android da iOS phones , danna 440 23# akan N200 kacal. _ Domin yin subscribing na daily airtel BBM plan akann android da iOS phones , danna 440 24# akan N100 cakal. NOTE:Ka sani cewa BBM kawai zaka iya yi da wannan bundle din kuma akan wayoyin android da Iphone ne. Don haka idan kana da tambaya zaka iya yi anan

YADDA ZAKAYI WHATSAPP KYAUTA AKAN LAYINKA NA AIRTEL.

YADDA ZAKAYI WHATSAPP KYAUTA AKAN LAYINKA NA AIRTEL. AIRTEL NIGERIA yanzu sunbada damar yin Whatsapp kyauta amma Free Trial… Kawai ka danna 948 1# akan layinka shikenan zaka cigaba da chat kyauta akan whatsapp dinka har lokacin daka cinye Free Trial dinka. Kuma zaka iya amfani dashi akan kowace waya kamar BLACKBERRY,ANDROID, iPHONE,JAVA j, SYMBIAN da sauransu… Kuma zaka iya yin browsing akan akan kowane app duk kyauta din..kamar irinsu..2go,facebook,opera mini,uc browSer da sauransu amma zakayi amfani da defult setting din airtel suka turo maki... Happy chatting.... Kowa ya ajiye numbersa ta whatsapp anan domin yin sharing din abubuwa na alkhari a cikin wannan watan ramadan mai zuwa..

ya'mace

CIWON YA'MACE NA YA'MACE NE Wata Amarya ce tayi dare, ta rasa abin hawa, sai can dare sai ga wani Direban babur ɗin Adaidaita sahu (keke Napep), ya taho ɗauke da wata Mata aciki. Amarya ta faɗa masa inda zata. Aka yi sa'a kuwa nan suka nufa. Amarya ta hau babur cikin fargabar, yau wanne irin faɗa Angonta zai yi mata. Don be fi sati biyu da bikin ba, ta tmby zuwa biki, gashi dare yayi mata. Amarya gabanta sai faɗuwa yake, tun tana zancen zuci har ya fito fili. Kira take "yau ban san abinda zan faɗawa Alasan zuciyarsa tayi sanyi ba. Na san dole ransa ya ɓaci. Ba ta ankara ba sai gasu sun ƙaraso inda za ta sauka. Dama gidanta a bakin titi yake. Sai ta ga Ango Alasan a ƙofar gida ya cika ya batse. Amarya ta sauka ta ƙarasa ƙofar gidan jiki a sanyaye. Alasan ya fara cewa cikin faɗa "sai ki koma inda kika fito........" Matar nan ta fito da sauri daga babur ɗin ta nufi Alasan tace "haba Alasan ya zaka faɗi haka? ta nuna Direban babur dama Kawu Mu'azu ne ya...

mace tagari

MACE TA GARI Wata rana wani talaka cikin magavata ya tsinci jaka a kasuwa, a lokacin kuwa basu da abin da zasu ci a gidansa, dan haka ya koma gida suka bude jaka da matarsa. Suna budawa sai suka ganta cike da Dinare, sai mijin yace Allah ya taimakemu arziki har gida,! koda matar taji haka sai tayi masa nasiha akan ya koma kasuwa, ya nemi me jakar ya bashi abinsa. Koda ya dawo ya gamu da me jakar, yayi masa cikakakken bayanin da ya tabbatar masa tasace, saiya maida masa kayansa.! Koda mai jaka ya karba sai yace masa:"malam kai talakane ko mai arziki", sai talakan nan yamasa bayaninsa a takaice, sai mai kudin ya miko masa jakar da dinaran yace dama wannan zakkatace ta bana na ware zan bawa wanda ya cancanta dan haka jeka na baka. Yaa Allah ka azurta mu da mata nagari masu halin kwarai...!

SAHABI BILAL

SOYAYYA ITACE: Lokacin da Sahaby Bilal (r.a) yakasa zama a Madeena, bayan mutuwar Manzo (S.A.W)..!!! -Domin duk sanda yafara kiran Sallah in yazo"ASH'HADU ANNA MUHAMMAD RASULULLAH" sai muryarsa ta shaqe saboda kuka....!!! Sai yanemi iznin Khalifa Abubakar (r.a) yakoma SHAAM yahadu da wasu Sahabbai acan.....!!! -Bai sakeyin kiran Sallah ba har saida yayi mafarki da masoyinsa (S.A.W) yace masa: HABA BILAL WACE IRIN BUSHEWACE HAKA?? SHIN LOKACI BAI YIBA DAZAKA ZIYARCEMU??). -Tuni Sahaby Bilal (ra) yadora siddin dokinsa sai madeena, yana shiga bai tsaya ko inaba sai masallacin Manzon Allah (S.A.W) yazauna gurin qabarin yanata kuka, harsai da jikokin Manzo (S.A.W) Hasan da Husain sukazo suka sameshi....!!! Suka rungumeshi suna goge masa qasa a jikinsa...!!! suka nemeshi Alfarma da yayi kiran Sallah...!!! -Sahaby Bilal (r.a) yatashi ya hau minbari yafara: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR 2...!!! -ASH'HADU ANLA ILAHA ILLALLAH....!!!: Tuni Madeena ta dauka da hayaniya da koke- koke....

ILU

Mallam Ilu ne yaje wurin wa'azi sai yaji mallam yana cewa duk wanda ya kwanta da matarsa, sau daya, kuma ya samu biyan bukata da ita toh ladansa a wurin Allah kaman ya kashe arna saba'in ne. Mallam Ilu yana dawo wa gida, sai ya samu matarsa luba tana gida tana dan wanke wanke, ya kirata Luba! Tace eh yace ashe a harkan ga alheri na sosai bamu sani ba? Luba tace wace harka? Sai yabata labari abinda Mallam ya fadi a wa'azi. Sai tayi kaman bata damu ba, Masha Allah dare yayi kaman yanda Mallam yayi bayani, Mallam Ilu ya kwanta da matarsa kwanciyar sunna ya kashe arna saba'in. Ya ja bargo ya rufa, chan dare matarsa Luba tace Ilu Ilu! Yache eh mi? Tace tashi ka kashe arna, Ilu ya tashi ya kashe arna saba'in. Ilu ya ja bargo ya rufe, chan tsakiyar dare ta tashe shi Ilu! Yace mi? Yace arna koh? Tace eh arna! Ya tashi ya kashe saba'in da kyar. Chan karshen dare ta sake tashinsa Ilu! Yace mi Luba? Tace arna! ya aje bargo gefe guda yace ke Luba waye sarkin yakin manzon Al...

harshenka

HARSHENKA ZAKINKA: 1. Harshe wata JAR TSOKA ce wacce Allah yayi maka ita cikin bakinka. Tana da mutukar amfani gareka wajen sanin Dandanon abubuwa da kuma bambancewa tsakaninsu. Bayan wannan Allah ya zuba baiwarsa mai yawa acikin wannan tsokar ta yadda zaka iya Lankwasata ka furta kalmomi tare da taimakon Makogoronka. Harshe shine yake fassara sakon da zuciya take daukr dashi.... Har ma wani lokacin saboda rigima irin na Harshe yakan furta abinda zuciyar ma bata Umurceshi ba. Harshenka kamar wani masifaffen zaki ne mai mutukar Qarfi akulle acikin bakinka, Idan ka barshi akulle, to ka Tsira daga sharrinsa.. Idan ka Sakeshi akan hanyar Alkhairi to kayi sa'a. Amma idan ka sakeshi ya farauci duk abinda yaga dama, to ka hallaka kanka da kanka. Domin kuwa acikin Minti guda zaka iya furta kalmar da zata janyi maka Shekaru dubunnai acikin Wuta. (Allah ya tsaremu). Ya Allah kasa mufi Qarfin Harshenmu da zukatanmu.

data

DAGA SAHLU BN SA'AD ASSA'IDY (RA) yace: "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa: "DUK WANDA YA LAMUNCE MIN (YA KIYAYE) ABINDA KE TSAKANIN LEBENSA GUDA BIYU (WATO HARSHE KENAN) DA KUMA ABINDA KE TSAKANIN CINYOYINSQ BIYU (AL'AURA KENAN), NI ZQN LAMUNCE MASA SHIGA ALJANNAH". (Imamul Bukhary ne ya ruwaito hadisin). DARASI : Acikin wannan hadisin Manzon Allah (saww) yana kwadaitar damu muhimmancin kiyaye harshe da kuma al'aura. Domin hakika mafiya yawan laifuffuka ana aikatasu ne ta hanyar amfani da wadannan gabobi guda biyu. Harshe dashi ake aikata shirka, dashi ake yin ridda, dashi ne mutum yake cin naman dan uwansa... Dashi ake mummunar rantsuwa, Kuma adalilinsa akan Kifa mutum acikin wutar Jahannama. Al'aura da ita ake zina, Madigo, Luwadi, Istimna'i da sauran abubuwan da Allah ya haramta.. Ga Azumi nan yana tafe, don haka duk wanda yake son ya samu cikakken ladan azuminsa, to sai ya kiyaye wadannan wurare guda 2. Amatsayinka/Amatsayinki na Daliban wan...

Wasanni

WASANNI: Brazil Ta Lallasa Kamaru Da Ci 4-1 Brazil ta tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa Kamaru da ci 4-1 yayin da Mexico ta doke Croatia 3-1 duka a rukunin A. Dan wasan Barcelona Neymar ne ya fara zira kwallo a minti na 17 kafin Joel Matip yafarke wa Kamaru a minti na 26. Neymar ya sake zira kwallo ta biyu a minti na 34 kafin Fred ya zira ta uku da ka tare da taimakon David Luiz sannan Fernandinho ya zira ta hudu ana dab da tashi.

tambaya

Assalamu Alaikum Malam. Allah Ya kara maka basira,amen. Meye matata zatayi amfani dashi wadda zai kara mata Ni'ima,saboda idan ina saduwa da ita wani lokaci tana jin zafi sosai idan ya dauke... Daga wani bawan Allah. AMSA * *** Yawancin daukewar Ni'ima yana faruwa ne ta dalilai kamar haka: 1. Cututtuka irin wadanda ake dauka alokacin Jima'I (STD). Da kuma cututtukan Mahaifa (disease of the womb). 2. Jinya matsananciya (har irinsu Malaria). 3. Rashin samun isasshen Abinci. 4. Shafar BAQIN ALJANI (Jinnul Ashiq). 5. Rashin kwanciyar hankali atsakanin ma'aurata. 6. Shan magungunan Asibiti (akwai wasu na'ukan maganin asibiti wadanda idan mace tana amfani dasu, to zata samu bushewar farji. Idan ta dalilin STD ne, ko kuma wata Cutar, to dole sai an magance cutar sannan ni'imarta zata dawo. Idan ta dalilin rashin kwanciyar hankali ne ko rashin abinci mai gina jiki, to da zarar an samu chanjin yanayi, to ita ma ni'imarta zata dawo. Idan ta dalilin Shan wasu Kwayoyi n...

nyako

Ana ci gaba da dambarwa a jihar Adamawa ta Najeriya game da yunkurin tsige Gwamna Murtala Nyako da wasu 'yan majalisar dokokin jihar ke yi. Majalisar dai ta sake zartar da wani kudiri da ya bai wa akawunta ikon sanar da Gwamnan da mataimakinsa sanarwar shirin tsige su ta kafafen yada labarai, bayan akawun ya kasa haduwa da su domin ya mika sanarwar hannu da hannu. Sai dai Gwamnan a nasa bangaren, ya ce 'yan majalisar sun sabawa ka'ida da zartar da wannan kudurin, saboda wata kotu ta riga ta haramta musu yin hakan, don haka ba zai saurare su ba. ''Mu wannan abin ya zamar muna abin takaici, abin dariya; muna ganin ya zama kamar ba wasan yara ba ma ya zama hauka,'' inji Ahmed Sajoh, mai magana da yawun Gwamna Murtala Nyako.

hanyar da shaitan yake halakar da mutane

. . 1,jahilci 2,fushi 3,son duniya 4,dogon buri 5,kwadayi 6,rowa 7,girman kai 8,riya 9,jijji dakai 10,hadama 11,son yabo 12,raki 13,son zuciya 14,mummunan zato 15,raina musulunci

soyyaya

***SOYAYYAR FACEBOOK*** Wani saurayi ne ya kamu da soyayyar wata budurwa a facebook wadda don tsananin soyayyarsu ta facebook ta sanya har suka yi rantsuwa tare da daukar wa kansu alqawarin auren juna a cikin duk irin yanayin halin da suka sami junansu don tsananin qaunar auren junansu da sukeyi ta sanyasu kullum chatting ba dare ba rana tare da yin waya kamar ba kudinsu suke qonawa ba inji Sa'ad Khalifa Yakubu (Sky) mai bada labarin sai suka shirya yadda zasu hadu da juna don a shirya ranar aure. udurwa taba saurayi adireshinta, shi kuma ya niqi gari takanas ta kano har garin budurwar. Yana isa gidan sai ya aika yaro a kira mashi budurwar sai yaron ya shiga da gudu, chan sai gata... Nan take fa saurayin nan ya rikice ya rude ya shiga kuka don saboda alqawarin auren nan da suka daukar wa juna. Toh wai me ya faru da har saurayin yabi ya kidime ne yake kuka? Na san irin wannan tambayar ke cikin zukatan mai karatu toh ba wata bace budurwar nan face naqasashshiya, gurguwa nannadaddiya ...

tambaya mabudin ilimi

assalamu alaikum Allah ya kara wa malam lafiya ameen tambayata anan itace ya hallata idan miji yana wasa da matarsa ya umurceta data tsotsan mai xakarinsa ko kuma idan suna kwance da matar sai mijin yakama tsotar wa matar farjinta. nagode malam (Daga wata Baiwar Allah). AMSA * *** A'a gaskiya ba za'a iya cewa Haramun bane kai tsaye saboda rashin Nassi wanda ya haramta hakan. Sai dai Mafiya yawan Malamai sun Karhanta yin hakan kuma Sunce yin haka ya kauce ma FITRAH (wato ainihin tsarin da Allah ya halicci bayinsa akai). Shaykh Nasiruddeen Albany ya buga wani misali: Yace koda acikin dabbobi babu wadanda zaka ga suna yin irin wannan alokacin Jima'I in banda aladu (Alhanzir). Kuma shi abisa fahimtarsa haramun ne Namiji ya sanya al'aurarsa acikin bakin Matarsa. Hakanan itama matar, haramun ne Namiji ya rika tsotsar Farjinta. Shi dai baki an halicceshi ne ajikin Dan Adam domin yin zikiri da karatun Alqur'ani da sallah da kuma addu'a da cin abinci.... Amma ba'a ha...

zabi

Saurin aure sai Mazan Bauchi 2. Gayu da rainin hankali sai Mazan Abuja 3. Kallon Mata sai Mazan Sokoto 4. Asirce Mata sai Mazan yobe 5. Bagu sai Mazan Gombe 6. Son harka da clubbing sai Mazan Kaduna 7. Matashi ga kudi da ilimi sai mazan kano 8. Kashema mata kudi kamar basusan zanfin nemaba sai Mazan Zamfara 9. Son karya sai Mazan Adamawa 10. Gidadanci sai mazan Niger 11. Zallar yaudara sai mazan Jos/Kogi 12. Anaso ayi wanka amma rashin kudi ya hana sai mazan Jigawa 13. Qauyanci da rashin wayewa sai mazan Kebbi/ Sokoto 14.ilmin Addini amma babu wanka sai mazan Borno 15. Soyayya da Rike Amana sai yan katsina 16. Qazanta da tarin dauda Sai yen Taraba... TRUE OR FALSE??

topa

NA RANTSE DA ALLAH GOODLUCK BAZAI QARA MULKIN SHUGABAN QASA A NIGERIA BA! Inji: Malam Abubakar Zubairu WALLAHI ALLAH BAZE KUNYATA RANTSUWA TABA SAIYA KUBUTARDANI, ZAN YI ADDU'A KAWAI KUCE AMIN,' YA ALLAH YA QAYYUM YA AZIZ YA JABBAR MUNA ROQONKA DA SUNAYENKA KYAWAWA DA SIFFOFINKA MADAUKAKA YA ALLAH KA SANYA MAKIRCIN GOODLUCK YA ZAMA SANADIN FADUWARSA A ZABEN BANA. YA ALLAH KA TONA MASA ASIRI SHIDA MUQARRABANSA YA ALLAH KA KUBUTAR DA AL'UMMAR MUSULMI DAGA QASQANCIN DA WANNAN SHAQIYYI YAKE JEFA SU CI YA ALLAH DA GAGGAWA. YA ALLAH KA AMSA MANA ADDU'AR MU A WANNAN LOKACIN AMIN KUCE AMIN DAN ALLAH.

wata rana

Watarana wani mutun yaje wajen wani malam, sai yace Mallam ni matashine mai tsananin sha'awa,kuma kullum ina cikin kallon mata a kasuwa,don Allah mallam ka bani shawara... Sai malam yayi shiru na dan lokaci,sai yace mishi ina zuwa. Ya shiga cikin gida ya dawo rike da kofi a hannunshi. Ashe madarar shanu cike fim a kofin kamar zai zube. Sai ya mika mishi,yace kafin in baka shawara zan aikeka, rike wannan madarar ka kaiwa wane a cikin kasuwa(ya mishi kwatancen wanda zai kaiwa).. Ya tashi zai tafi, sai malam yace amma akwai sharudda akan wannan madarar. Bana so ko digo daya ya zuba a kasa,idan kuma ya zuba,ga almajirina zaku tafi tare dashi, yana binka a baya da tsumagiya,idan yaga digo daya ya zuba a kasa zai shauda maka ita da karfinsa..Sai mutumin yace Mallam bazan barima ya zube ba! Cikin sa'a kuma sai ya kai madarar ba tare da zubar da digo ba..Ya iso ga Mallam cikin murna yace na isar da sako yadda ka umurceni. Sai Sheik yayi murmushi yace,akan hanyarka ta zuwa fuskokin muta...

wasu kwadi su 2

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau kuma mun zakulo wani tsohon labari ne, wanda ke cike da darussan rayuwa, musamman ma ta fuskar turzawa ko yin kokari a rayuwa. Labarin dai ya kasance ne na wasu kwadi guda biyu, daya yana da kiba sosai, daya kuwa ramamme ne, marar kumarin jiki. Wata rana suna kiciniyar neman abinci a wani kamfanin yin madara, sai kaddara ta sanya suka fada cikin wani durum din madara. Suka yi kokarin su fita daga cikinsa, amma dai suka kasa, musamman saboda gefen durom din santsi ke gare shi, don haka duk yunkurin da suka yi domin fita, sai santsin nan ya tadiye masu kafafu su sake fadawa. Suna cikin kiciniyar fitowa, sai kwadon nan mai kiba ya ce wa ramammen: “Ya kai dan uwana, ina ganin mu daina bata lokacinmu a banza, domin kuwa mun riga mun halaka. Mu daina yin wani kokarin fita, domin kuwa babu wata hanya da nake ganin za mu kubuta.” Shi kuwa ramammen kwadon nan, kasancewarsa mutum mai kokari, sai ya ce wa dan uwansa:...

koliya datsafta

KWALLIYA DA TSAFTA A CIKIN AZUMI Kwalliya da tsafta a cikin Azumi, marhaban lale azumi na hanya ya kusa saura qiris, kuma muna farin ciki da shirin zuwan sa. Wannan ne dalilin da ya sa na ga ya dace na yi magana a kan irin kwalliyar da ta dace da wannan wata mai albarka, da kuma yadda ya kamata ki tsaftace gida da jiki. Tsaftar muhalli dai kowa ya san abu ne mai kyau ga xan adam, saboda haka yana da kyau uwargida ta tsaftace muhallinta da canja duk wani abu da ki ka san ya tsufa da sabo balle ma wajen girki. In kuma babu halin canjawa sai a gyara ko ina, ko a canja musu wuri a xauke daga wurin da su ke da su koma wani sabon wurin, saboda shi zai qara wa kitchen xin da xaki kyau da martaba ban da tara tarkace, xebe shirgi da adanawa na gyara gida da canja labulaye. Ina qara jan hankalin mata kar kice ni bani da shi saboda haka ba zan gyara ba, da wanda ki ke da shi xin zaki gyara don mijinki ya ga canji, ki sani su maza ‘yan son su ringa ganin sabon abu ne don yana qara sa su ji daxi da...

niimar allah

Wani mutun ne ya ga hadari ya hadu, gari ya yi baki kirin sai ya kama hanyar gida yana ta sauri. Sai suka hadu da wani mutum, ya ce: “Malam, ni’imar Allah za ta sauka kake gudunta?” Sai mutumin nan ya daina sauri, ruwan ya sauka ya yi masa dukan tsiya. Rannan yana zaune sai ya ga wannan mutumin da ya hana shi sauri yana ta sauri saboda ya ga hadari. Ya ce: “Malam rahama za ta sauka kana gudunta?” Sai ya ce: “Ina gudu don kada in taka rahamar ne.”

saikai

A wani otel ne a Hadeja, aka rubuta a jikin allon sanarwa cewa: “Ka ci, ka sha iya yinka, amma jikanka ne zai biya kudin. Wani Bakatsine da ya ga haka, sai ya shiga otel din, domin dai ya san cewa ba shi ma da aure balle jika; wato zai ci banza ya tafi. Bayan ya ci abinci ya gama, sai ya ga daya daga cikin ma’aikatan otel din ya kawo masa takardar adadin kudin da zai biya. Bakatsine ya ce: “Ya haka? Ku fa kuka ce jikana ne zai biya kudin.” Ma’aikacin ya ce masa: “Ai da ma ba kudin da ka ci ne za ka biya ba, na kakanka ne da ya ci za ka biya, ga shi can a zaune.”

topa

*SHEDAN YACE: * 1- wanda duk yana jin kiran sallah amma baya zuwa masallaci to babana ne 2- matar da duk bata so taji anyi sallama a gidanta, to uwatace 3- wacce duk bata suturta jikinta, to matata ce 4- wanda duk yake riga liman sajada ko ruku‘u to yarona ne 5- wanda yake fara cin abinci ba basmala to tare muke ci 6- wanda ya taimaki wani yayi shahada, wannan makiyi nane

dolle adaina shigo da janareta nigeria taron kasa

A farkon makon nan ne wakilan taron kasa da ke gudana a Babban Birnin Tarayya Abuja suka yi kiran a dakatar da shigo da injunan bayar da hasken lantarki na janareta bakidaya a kasar nan a matsayin wani kwakkwaran mataki na habaka bangaren lantarkin kasar wadda ya kasance cikin mawuyacin hali tun da dadewa. Wakilan sun yi kiran ne a sa’ilin da ake tattauna rahoton kwamitin da taron ya kafa a kwanan baya a kan makamashi. Sun bayyana cewa ci gaba da sayo injunan janaretan daga waje yana dakushe kokarin wadata kasar da ingantacciyar wutar lantarki. Daya daga cikin wakilan, Chris Abongabe ya nunar da cewa idan Nijeriya za ta sanya gawayi a cikin abubuwan da take amfani da su wajen samar da makamashi, za a samu kyakkyawan sakamako. Wakazalika, ya bukaci taron ya nada wasu wakilai su ziyarci kasar Ghana da Afirka ta Kudu da za su rabe tsaki da tsakuwa don gano musabbabin abin da yake tarnake habakar makamashin Nijeriya. Shi kuwa Barista Abubakar tsokaci ya yi kan cewa akwai fa lauje cikin nad...

garabasa

GARA6ASA GA DUK MAI AMFANI DA LIYIN MTN Sanin kowane idan mai amfani da layin mtn xai sai 10mb sai yanada naira 100 TOga gara6asa da xaran kasa kudi a wayarka sai ka danna 216 7# ZASU kwashe naira 70 KACHAL subaka mb goma

abbin mamaki

WANI ABIN DAUSAI YA FARU DA WATA YARINYA KWANAN NAN WATA YARINYA TA SHIGO MOTA TARE DA FASINJA ZUWA KEBBI SAI TACE MA DIREBA INA SON INYI FITSARI BAYAN SUNZO TSAKANIN SOKOTO DA KEBBI SAI DIREBA YA TSAYA FASINJA SO KA SAUKA SAI YARINYAR TAJE TAYI FITSARI GAMA FITSARINTA KEDA WUYA TAJUYA TA SHIMA MOTA SA KAWAI DAJI IDANUWANTA SUNRUFE BATA GANI TA MAKANCE YANZU HAKA TANA GIDA TAZAMA MAKAUNIYA DON ALLAH DUK WANDA YAGA WANNAN POST YA TAYATA DA ADDU'A ALLAH YA WARKAR DA ITA YAMAYAR MUTA DA GANINTA NA DA YA BATA LAFIYA ALLAH AMEEN.

android unlock key

YADDA ZAKA BUDE KO RESET DIN SECURITY CODE DIN WAYAR ANDIRIOD BAYAN AN MANTA !! A Yau yawancin Mutane Suna Amfani da waya Kirar Andiriod Dan Amfanin kansu.Hakan ne Nema yasa Wasu Lokuta Wasu ke Sa Security Code A wayar Tasu, Domin su Tsare wayar Tasu Daga Muta Ne Saboda Mantuwa Ko kuma mu iya Cewa Harkoki Sunma Wasummu Yawa Saikaga Mutum ya manta ko Meya Seta A Matsayin Pasword din nasa Daga nan kuma Sai a shiga Ruda ni Sai ankaita Anyi UNLOCKING dinta Inma Anyi Rashin Sa'a Saikaji Ance sai Anmata Flashing..... Idan kaima kasamu kanka cikin wanda yasa Security Code Na Wayarsa Kirar Andriod, Kuma ya manta Toga Mafita Inkabi Wadannan Matakai.... Mataki Na Farko : Ana bukatar Ka kase wayar Taka Mataki Na Biyu : Saika danna key din Volume Na Sama Yayi tsahon 30 Seconds Mataki Na Uku : Saika danna Home Buttom Wato key Din Shiga Menu din wayar kenan Saika Danna Key din Kunna wayar A tare Har sai wayar Takawo, Tana kawowa saika SakeY key din da ka danna Wato Home Key Da Switch Key Mataki ...

wata rana

" Wata rana wani mutum yazo wajen Wani Malami domin ya warware masa matsarlar cikin gidansa. Yace, Malam inada matata mun dade tare, kuma muna da yara, amma yanzu sam bana jin sonta da sha'awarta a cikin zuciyata. Sai Malami yace, mai yasa baka sonta ?Ta canja fasali ne ko tayi kiba dayawa ?Sai mutumin yace a'a, tana nan kamar yadda take kafin in aureta. Malami ya sake cewa ko kuma tasamu nakasa a dalilin wani hatsari? Yace ko daya Malam.. Can sai Malamin nan yace dashi. Hakika zuciyarka ta karfafa wajen kallon matan waje da suke wucewa,sannan kuma kana shagalta da kallon hotunan batsa. Nan da nan mutumin mamaki ya kamashi. Ya sunkuyar da kai, yace Malam wannan zance haka yake. Amma yaya akayi kagane hakan tattare dani? Sai Malamin yace: "Idan har zuciyarka ta dulmiya zuwa ga Haram, ko kana cin Haram, ko kana mu'amala da abubuwan Haraam, ko shakka babu zaka zama mai gujewa "HALAL". Ya Allah ka kiyaye zukatanmu daga aikata alfasha.

saunawa kagaisar da manzo (saw)

SAU NAWA KA ZAUNA DOMIN GAISAR DA MANZON ALLAH (SAWW) ??? Akwai Ingantaccen Hadisi daga Manzon Allah wanda ya nuna cewa akwai Mala'ika akan Qabarinsa wanda yake isar masa da gaisuwar al'ummarsa gareshi. Sannan kuma duk ranar Juma'ah ana dawo masa da ransa cikin jikinsa, Kuma babu wani wanda zai gaisheshi fache sai ya amsa masa da kansa... Shin ba zaka ji dadi ba, ache ka gaisa da SHUGABAN HALITTUN ALLAH BAKI DAYA?? (SAWW). Ni dai ga tawa gaisuwar nan YA RASULALLAHI.. "Assalamu alaika ayyuhan Nabiyyu wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuhu". Assalatu wassalamu 'alaika ya Rahmatallahi. Assalatu wassalamu 'alaika ya Safwatallahi. Assalatu wassalamu 'alaika ya Habiballahi.. Sallallahu 'alaika wa 'ala aalika wa Sallam.

dan audu

Image
ALLAH ya rahamamaka sankano

bukin mata na duniya

Image
Wannan gungun jamaa ne yayi bukin mata na duniya daaka gudanar a new

sorry naija

Image
Kash banda lokacin gyara naija sorry

ikon

Image
ALLAH mai yada yaso da bawanasa allah kadatar damu

WASANNI: Okocha Ya Caccaki Keshi

WASANNI: Okocha Ya Caccaki Keshi Daga Suleiman Idris. Tsohon dan wasan Nigeria Austin Jay-Jay Okocha ya dora alhakin rashin cin kwallon da ‘yan Nigeria suka yi a wasansu da Iran a kan mai horas da ‘yan wasan na Super Eagles Stephen Keshi. Jay-Jay Okocha ya ce kamata ya yi Nigeria ta lashe wasanta da Iran amma kasar ta gaza yin hakan. A cewar Okocha, Keshi bai yi aiki sosai ba akan ‘yan wasan, kuma ya yi kuskure da ya sauya Bictor Moses da Shola Ameobi bayan hutun rabin lokaci. A ranar asabar ne Nigeria za ta buga wasanta na biyu da kasar Bosnia-Hercegobina, wacce ta sha kashi a hannun Daga Suleiman Idris. Tsohon dan wasan Nigeria Austin Jay-Jay Okocha ya dora alhakin rashin cin kwallon da ‘yan Nigeria suka yi a wasansu da Iran a kan mai horas da ‘yan wasan na Super Eagles Stephen Keshi. Jay-Jay Okocha ya ce kamata ya yi Nigeria ta lashe wasanta da Iran amma kasar ta gaza yin hakan. A cewar Okocha, Keshi bai yi aiki sosai ba akan ‘yan wasan, kuma ya yi kuskure da ya sauya Bictor Moses d...

maganin ganin annabi (saw)

#MAGANIN_GANIN_ANNABI_(SAWW) Wani mutum yazo wajen SHEHU USMAN 'DAN FODIO (rah) yace masa "Modibbo nazo wajenka ka bani Maganin ganin Annabi (saww) domin kuwa tunda nake ban ta'ba mafarkinsa ba, duk da cewa ina yawaita salati gareshi". Sai Shaikhu 'Dan Fodio yace masa "Idan kaje gida kace ma Matarka ta dafa maka WAKE, ta sanya maka mai Sosai, amma idan ka gama ci, kar kasha ruwa.. Kaje ka kwanta. Duk mafarkin da kayi, kazo ka gaya min, dashi zan hada maka maganin ganin Annabin (saww)". Wannan mutumin ya tafi gida yasa Matarsa ta dafa masa wake, yaci ya Qoshi, har zai sha ruwa, sai ya tuna cewa Shehu yace masa kar yasha ruwa. Don haka sai kawai ya tafi ya kwanta barcinsa. Tunda ya kwanta sai Mafarke-mafarke yake tayi. Amma duk mafarkin nasa bai wuce kan abu guda ba... Wato SHAN RUWA. Sai yayi mafarkin cewa yazo bakin rijiya ko bakin rafi yana shan ruwa mai sanyi. Da ya farka da asuba, yaje yayi sallah sannan ya wuce wajen Shehu 'Dan Fodio domin ya bas...

asara ranar jumaa

{ WADANDA SUKAYI ASARA RANAR JUMA'A } 1 wadanda basa zuwa massalaci da wuri.. Sunyi asarar ladan sadakar rakumi 2 wadanda suke magana liman na hudu ba.. Basuda ladan juma'a saidai azahar. 3 wadanda basajin larabci sunyi a sarar fadakarwar liman in baya fassara huduba. 4 wadana suke sallah a gaban liman sunyi a sarar sallar. Matukar bayansu akwai sauran sahu. 5 wadanda ke taruwa don lazimin juma'a sunyi asarar lokacin su lokacin juma'ar kuma ya kubuce. 6 wadanda ke tafiya massalaci kan motoci da babura sunyi a sarar falalar kankare musu zunubbansu. 7 wadanda basa kure adaka da sanya turare sunyi a sarar koyi da ANNABI (saw) 8 marasa aure ladan saduwa da iyali gabanin fita massallacin juma'a yayi musu fintin kau.. Ya ALLAH karabamu da asarar duniya da lahira ameenn.. Ya ALLAH kasa kowannen mu yadace da sa'ar karbar addu'a dake cikin wanan rana.. Ammeeenn naku Abubakar lawal yake maku barka da wanan rana mai daraja..

zikirin fitowa daga gida

ZAUREN FIQHU ZIKIRIN FITOWA DAGA GIDA * ************************* Duk wanda yake bukatar samun Cikakkiyar kariya daga sharrin ALJANU DA MUTANE, tare da kiyayewa da shiriyar Allah acikin dukkan lamarinsa, to aduk lokacin da zai fito daga gidansa zuwa wajen aiki ko kasuwa, ko masallaci, ko balaguro zuwa wani garin, SAI YACE: ''BISMILLAHI TAWAKKALTU ALAL- LAHI. LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL-LAH'' FASSARA: (zan fita) da albarkar sunan Allah, ga Allah na dogara. babu wata dabara ko wani Qarfi sai daga Allah'' Duk wanda ya fadi wannan zikirin Qafa daya yayin fitowarsa daga gida, Mala'ikun Allah zasu ce masa: "AN RIGA AN ISAR MAKA (daga dukkan sharri) kuma an shiryar dakai, kuma an kare ka". Nan take, shaitan zai kauce daga wajensa, sai wani Shaitanin yace ma babban nasu "YAYA ZAKAYI DA MUTUMIN DA AKA RIGA AKA SHIRYAR DASHI, KUMA AKA ISAR MASA, AKA KUMA KARESHI?" (SAHIHUN: Abu Dawud ne ya ruwaitoshi acikin Kitabul Adab, hadisi mai lamba 5,095. ...

bani isra'il

Anyi wani Mutum mai sabon Allah a cikin Bani Isra'ila, iyalan shi suka fadakar da shi a kan ya daina sabon Allah amma bai fadaka ba. Sai Allah yayi wahayi zuwaga Annabi Musa(alaihi ssalaam) bisa cewa: ya fitar da wannan mai sabon Allah kada azaba ta same su. Sai wannan Mai sabo ya bar wannan gari zuwa wani. Sai Allah ya umarci Annabi Musa (alaihis salaam) da ya je ya fitar da shi daga wannan gari. Sai wannan mutum ya tafi wani kogon dutse ya tare a ciki yana mai tuba zuwaga Allah. Sai Mutuwa tazo ma wannan mutum, sai yake cewa: Wayyo Allah! Da Mahaifiyata tana kusa da ta taimaka mani, kuma da tayi mani kuka saboda halin da nake a ciki. Wayyo Allah da Mata ta tana kusa da tayi mani kuka saboda halin da make ciki, haka yaya na da. Wayyo Allah da Babana yana kusa da yayi mani wanka! Ya Allah! Kamar yadda ka yanke tsakanina da iyali na, kada ka yanke ni daga rahamar ka. Ya Ubangiji kada ka kona ni da wutar ka saboda sabo na. Nan take sai Allah ya turo Hurul'ini a cikin surar Mahaif...

hadith

↓ Sahihin Hadisi Daga Cikin SAHIHUL MUSLIM, Daga Sahabi Abu Zarril Giffari Ya Ce:- "Watarana Muna Zaune Tare Da Manzon ALLAH(S.A.W) Da Yamma, Sai Rana Ta Tafi Zata Fadi Sai ANNABI(S.A.W) Ya Ce: 'Ya Abu Zarr Ko Kasan Inda Ranar Nan Zata Fadi???' Sai Abu Zarr Ya Ce: ALLAH Da Manzonsa Ne Sukafi Sani, Sai ANNABI(S.A.W) Ya Ce: Ai Ba Faduwa Takeyi Ba, Tana Zuwa Gaban ALLAH (S.W.T) Ne, Sai Ta Fadi Tayi Sujjada Ga ALLAH(S.W.T) Idan Tayi Sujjadar Sai ALLAH Ya Bata Dama Sai Ta Wuce, Shine Sai Ta Bullo Ta Gabas Idan Gari Ya Waye, To Ana Nan Watarana Zata Je Tayi Sujjada Gaban ALLAH Sai ALLAH Ya Ce:- An Karbi Sujjadarki Amma Yau Ba Za'a Baki Hanya Ba, Ki Koma Ta Inda Kika Fito, Idan Ta Koma Kuma Gari Ya Waye Sai Ta Bullo Ta Yamma...... To a Wannan Lokacin Ne Fa Da Zaran Rana Ta Bullo Ta Yamma To An Rufe Kofar Karbar Tuba Babu Wani Wanda Zai Tuba ALLAH Ya Karbi Tubansa Kuma a Wannan Rana Ne Ko Da Kafiri Ya Ce LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH (S.A.W) To ALLAH Ba Zai Karbi...

Tofa wani kaya sai amale

MATAN AREWA???? HAUSA @ Idan kana neman MATA wacce baza ta zage ka ba, ko cin mutunci, Amma akan abu kadan sai ta zagi har kakannin ka na farko, Kuma ba godiyar Allah, To auri BAHAUSHIA FULANI @ Idan kana son MATA mai kyau, Amma bata iya GIRKI ba, To auri BA FULATANA SHUWA @ Idan kana son MATA mai kyau, Da ladabi, amma kuma duk abun da zatai maka dan KUDI ne, To auri SHUWA BABUR @ Idan MATA kake nema, Wacce zaku dunga chasuwa kamar yan BOXING, To auri BABUR NUPE @ Idan so kake ka AURI MACE, Saboda tsabar BIYAYYA kamar tayi maka BAUTA, To ka auri BANUFIYA MARGI @ Idan kana son MACE mai kyau, Amma ta tsani BEST FREIND dinka, To auri MARGI GWOZA @ Idan kana son wacce baza ta ta6a barin ka kai motsi ba, Ko da kayi shekara hamsin (50) da sakin ta, Auri yar gwoza KANURI @ Idan kana son mace mai kula, Da iya soyayyah, Amma duk sai ta kori matan ka, Idan kuma ka aure ta, babu, ba kai ba qara aure To auri KANURI BAZAZZAGIYA @ Idan kana neman mata local, Wacce baza ta ta6a chanzawa ba, ko mae ka...

falalar Azumi

FALALA ASHIRIN (20) TA WATAN RAMADAN 1, A cikin sa aka saukar da Alkurani mai girma, Bakara 185 2, Dukkan littafan Allah mai girma, a cikin sa aka saukar da su, takardun Annabi Ibrahim a daran farko na watan, Attaurar Annabi Musa a ranar 6 ga watan, Injilar Annabi Isa 13 ga watan, Alkur'anin Annabi Muhammad saw, a ranar 24 ga watan, Musnad Ahmad, shaik Albaniy ya ingantashi. 3, Ana bude Kofofin Aljannah a cikin watan, 4, Ana rufe kofofin wuta 5, Ana daure kangararrun shedanu 6, Ana bude kofofin Rahma 7, Ana bude kofofin sama 8, mai kira yana kira, ya mai neman alkhairi gabato, ya mai neman sharri, kayi nisa 9, A ko wanne dare, Allah yana yanta bayi daga wuta 10, A cikin watan akwai daran lailatul kadri wanda yafi wata dubu, 11, Ana kankare zunubin shekara, Annabi saw yace, Daga Ramadana Zuwa Ramadan aka kankare zanubi duka, mutukar an nisaci kaba'ira 12, An durmuza hancin, Duk wanda Ramadana ya kama har ya wuce baiyi aikin da zaayi masa Rahma ba. 13, Umra a cikin watan Ramadan ...

manzo (saw) yacce

MANZON ALLAH (S.A.W) YACE 'DABI'UN ALHAIRI GUDA DARI UKU DA SITTIN NE(360) SAI SAYYIDINA ABUBAKAR YACE> YAMA'AIKIN ALLAH INADA DAYA DAGA CIKINSU? SAI ANNABI (S.A.W) YACE DIK GABAYANSU KANA DASU YA ABUBAKAR(IBNU ASAKIR YA RUWAITO) A WANI HADISIN ANNABI (S.A.W)YACE KAUNAR ABUBAKAR DA GODE MASA WAJIBI NE AKAN DUKKANIN AL'UMMATA(IBNU ASAKIR NE YARUWAITO) A WANI HADISIN ANNABI (S.A.W) YACE DUKKANIN MUTANE ZA'AYI MUSU HISABI AMMA BANDA ABUBAKAR(ABU NA'IM YA RUWAITO)SAYYIDINA UMAR YANA CEWA IN DA ZA'A GWADA IMANIN ABUBAKAR DA IMANIN ABUBAKAR YARINJAYI NA SAURAN MUTANE.(BAIHAKI NE YARUWAITO) KUMA SAYYIDINA ALIYU YACE NA RANTSE DA WANDA RAINA YAKE HANNUNSA,BAMU TA6AYIN TSEREN AIKIN ALKAIRI BA,FACE SAI ABUBAKAR YA TSEREMANA.(DABARANI NE YA RUWAITO) KUMA SAYYIDINA ALIYU YACE MAFIYA ALKHAIRIN MUTANE A BAYAO MANZON ALLAH SUNE ABUBAKAR DA UMAR KAUNATA BATA HADUWA DA KIYAYYARSU(DABRANIY YA RUWAITO)

assalamualaikum

Assalamu alaikum warahmatullah, Yan uwa barkanmu da saduwa a wannan littafi mai albarka na Umdatul-Ahkam, a darasin daya gabata mun tsayane a hadisi na 63 a BABIN FALALAR SALLAR JAM'I, ayau kuma da yardan Allah zamu ci gaba: 64. An karbo daga Abu-Hurairah R.A yace: Manzon Allah s.a.w yace: Mafi Nauyin Sallah ga Munafuqai itace: Sallar ishaa'I da Alfijr, Da ace sunsan abin dake cikinsu (na falala) da sunjesu koda da jan ciki ne, haqiqa na himmantu akan na Umarcesu da sallah, sai a tayar da ita, sannan na Umarci mutum, yayi sallah tareda Mutane, sannan na tafi da wasu daga cikin mazaje, tare dasu su daukamin itatuwa, mutafi ga mutanen da basu halartan sallah, sai in qone gidajensu da wuta. 65. An karbo daga Abdullahi bn Umar R.A, Daga Manzon Allah S.A.W yace: Idan Maatar dayanku tanemi izininsa zuwa masallaci, to kada ya hanata. Ya ce: sai Bilaal bn Abdillaahi yace: Na rantse da Allah sai mun hanasu. Yace: sai Abdullahi (bn Umar) ya fuskance ya zageshi zaagi mai tsanani, ban taba...

labarai

Jagoran Musulunci A Kasar Yarbawa Ya Rasu Rahotanni daga birnin Ibadan babban birnin jihar Oyo ya tabbatar da cewa fitaccen dan kasuwan nan kuma jagoran addinin Musulunci a jihar Abdulazeez Arisekola Alao ya rasu a jiya a wani asibiti da ke kasar Switzerland. Wata majiya daga iyalan mamacin ta bayyana cewa mamacin ya rasu ne sakamakon ciwon kansa, sannan kuma ana shirin kawo gawar Nijeriya domin yi masa jana'iza a gobe da safe kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. A shekarar 1980, wata kungiyar malaman Musulunci sun ba shi mukamin 'Aire Musulumi Of Yorubaland, ma'ana uba ga Musulman kasar kabilar Yarbawa, wanda hakan ya ba shi zama daya daga cikin masu yi wa addini hidima a yankin kasar Yarbawa. Bayan kasancewarsa hadimin addinin Musulunci a Nijeriya, marigayin hamshakin dan kasuwa ne. An haifi marigayi Alao a 1945, inda ya fara harkokin kasuwanci a matsayin dan tireda har zuwa lokacin da Allah ya nufa ya zama cikakken dan kasuwa. Sannan kuma ya rasu ya bar mata da yara...

Niyyar yin jima'i

NIYYAR GABATAR DA JIMA'I Sahabin manzon Allah (s.a.w) ya fada a cikin wasiyyarsa cewa. "A lokacin gabatar da jima'i, ya kamata ango ya daura wadannan niyyoyi." 1. Ango ya daura niyyar Kare kansa daga zina. 2. Da niyyar kare kansa daga kallon matan da ba halal din sa ba. 3. Da niyyar samar da "ya"ya na gari wadanda zasu yiwa Musulunci hidima. Idan har ango ya gabatar da jima'i da amaryarsa tare da kyakkyawar niyya ya sami gamsuwa da ita akwai lada da Allah madaukakin sarki zai bashi wannan na nuni ne da muhinmmancin sanya kyakkyawar niyya a zukata kafin saduwar jima'i, kuma ana samun falala daga wannan niyyoyi kyawawa, an so a lokacin da ango da amarya ke shirin saduwa da juna su ta6e tufafinsu sannan su lullu6a, su kashe fitila, kamar yadda aka samo cikin wani hadisi, Jabir bin Abdullahi, Allah ya yarda dashi yace; Manzo (s.a.w) yace idan duhun dare ya gabato ko kuma almuru tayi to ku hana "ya"yanku fita. Domin shaidanu suna bazuwa a wannan...

assalam

LITTAFIN UMDATUL-AHKAM Assalamu alaikum warahmatullah, Yan uwa barkanmu da saduwa a wannan littafi mai Albarka, Idan baku mance ba, a darasin da ya gabata, mun tsayane kan bayani gameda hadisi na 65, Cikin BABIN FALALAR SALLAR JAM'I DA KUMA WAJABCINTA: Hadisin da Abdullahi bn Umar yake cewa: Manzon Allah S.A.W yace: (Idan Dayanku matarsa tanemi izininsa don zuwa masallaci, to kada ya hanata). A wata ruwayar kuma Annabi S.A.W yace: (Kada kuhana bayin (mata)Allah daga gidajen Allah). Wannan Hadisi shine wanda kai tsaye ya bawa Mata Yanci da damar zuwa Masallaci suma suyi sallah a ciki, kuma wannan hadisi ya game dukkan mace, daga Yarinya, Budurwa, tsohuwa, Matar Aure, bazawara, kuma bai kawo wani sharadi ba ko qa'ida na yanda matayen zasu kasance, tun daga Fitowarsu daga gidajensu, har zuwa halin da zasu kasance a cikin Masallacin, Hakan Yasa Malaman Fiq'hu suka Kawo Sharudda da Qaa'idoji, Wanda Dolene Mace ta cikasu kafin taje Masallaci, sune kamar haka: 1: Kada ta sanya...

dabiun musulmi na kwarai

DABI'UN MUSULMI NA QWARAI // 10 Da yawanmu mun sani cewa son Annabi ibada ne, don kuwa duk abin da yake imani bai samuwa sai da shi haqiqa ya zama bauta, wannan ya sa wasu in za su roqi mutum wani abu suke cewa don Allah don son Annabi, soyayya gare shi kam kyakkyawar dabi'a ce da kowani musulmi ya zama wajibi ya sifantu da ita, dubi dai abin da Annabi SAW ya ce: لا يؤمن أحدكم حتى أكون أحب إليه من والده وولده والناس أجمعين Dayanku ba ya zama mumini sai ya fi qaunata sama da mahaifinsa da mahaifiyarsa da daukacin mutane. BUKHARI Tunda qaunar Annabi ta zama sharadi na samun imani, haqiqa ta zama dole a duk nau'o'in ibada da mutum zai yi, dubi dai yadda kubutar da iyali ta zama tilas a kan mumini, haka fifita qaunar Annabi ma ta sami wannan matsayin, Annabi SAW ya ce: لا يؤمن عبد حتى أكون أحب إليه من أهله وماله والناس أجمعين. Bawa bai zama mumini sai ya fi qaunata sama da iyalinsa da dukiyarsa da daukacin mutane. MUSLIM kenan ba sauran fakewa da qaunar Annabi wajen yi wa w...

S.A.W

Annabi Muhammad (SAW) .. da Nana Aisha (RA) Wata Rana Nana Aisha R.A suna zaune da manzon Allah (S.A.W), Ta kura masa ido tana kallonsa, Can sai tace ya Rasulillahi wai don Allah yaya wannan yusuf din yake da akace mata saboda tsaban kyansa in sun ganshi har yanka hannayensu suke??? . Kawai sai manzon Allah (S.A.W) ya bude tafin hannunsa mai Albarka kawai ya nuna mata fuskan Annabi yusuf, yace mata ga yusuf din,sai Nana Aisha tai murmushi tace wani abu sai mata inama baku yanka hannayen kuba, kuzo kuga shugaban kyawawa, Ta kara dacewa ya Rasulillahi wallahi tafin hannun nan naka yafi fuskan Annabi yusuf din kyau. .. . SALLAL LAHU ALAIHI WASSALAM. YA ALLAH KASADA FUSKOKINMU DA WANNAN KYAKYKYAWAN FUSKA.DON GIRMAN ALQUR'ANI AMEEEEEEEEEN. @[174223056110540:0]

hmmm mata kenan

SHIN WAI HAKAN ZATA IYA FARUWA KUWA......??? KHADIJAT:.. Assalamu alaikum. KHABEER:.. (ya kalleta da gefen ido) Wa alaikissalam. KHADEJAT:.. Don Allah idan bazaka damuba minti biyu mana. KHABEER:.. Gaskiya sauri nake banason bata lokaci. KHADEJAT:... Don Allah kayi haquri wata magana mai mahimmanci nakeson muyi dakai. KHABEER:.. Ina sauraronki (ya daga kai sama) KHADEjat: ..Haqiqa dabi'unka da riqon addininka sun dade suna birgeni, a kullum Naganka sai naji sonka yana qara mamaye zuciyata, idan bazaka damuba inaso ka bani sararin acikin zuciyarka domin na samu nakasa hajata, kuma na tabbata zanci ribar soyayya da Kaunar a cikin zuciyarka. KHABER:.. (ya danyi murmushi) gaskia ku 'yanmata ba abin yarda bane, sai mutum yabaku dama sai ku yaudareshi ku barshi acikin damuwa. KHADEJAT:... Haba ya za'ayi na yaudari kyakkyawan saurayi kamarka? Ai ba duka aka taru aka zama dayaba, wallahi sonka nakeyi har zuciyata, akullum da tunaninka nake kwana nake tashi. KHABEER:... To sai nayi ...

World cup Vs Ramadan

Image
"WORLD CUP vs RAMADAN" Dear brothers and sisters in islam. This year(1435/2014) will be a year of # FITNAH in our IBADAHT. World cup commences on 12th june 2014 where as Ramadan could begin 28th june 2014. Ramadan is a special Month while world cup is just a game of wasting time. if each game is 90 minutes and Ramadan will have 15 days consumed in world cup then you will have lost 1350 minutes watching world cup. ( assuming you only watch one game a day). Assume you spent 1350 minutes memorizing Qur'an,listening Darasah,doing more of istighfar reading ahadeeth you will earn oncountable rewards... my dear brothers and sisters in islam we need more Taqwah than world cup,let us wake up and not waste time ! this is the month of Ibadah. Don't be temted to miss the fruits of Ramadan,it may grant you Jannah(Al-Rayyan) while world cup will make you stressed,unhappy because your Team has lost ! Allah ta'ala Guide us all and grant us Al- Rayyan.

soyyaya

KYAKYAWAN TUNANI...... irin na masoya Hakika ina mai takama da masoyiya managar ciya acin duniyar masoya wadda tasan sirrin. kauna gaba kidayanta wato ke kenan masoyiyata... Hakika tun tuni batun yauba farashin sonki yakara hauhawa acikin zuciyata hakan yasan ya yanzu banida wata tamkarki ko wad da tafiyeminke atakaice dai ke nake kauna masoyiyata tabbas daga kanki narufe zuciyata don gudun shigar son wata banida tam karki zuciyata daga maman ummi sai ke sahibata masoyiyata na mallaka miki ruhina baki daya domin kuwa zan iya aiwatar da komai dan kare martabarki acikin taron masoyana duniya sahibata kiyarda dani idan na cedake kishirwar son ganinki tare da karancin jin sautin zazzakar muryarki kan jirkitar da kamannin jikina daga yanayin farin ciki yazuwa yanayin tabba tacciyar kauna zuwa gareki mai sanyani jin ko alama bana tunanin da akwai wani abu da ya isa ya iya girgiza zuciyata sonki dake acikin ruhina yafi dan karamin tunani dan aduk lokacin danayi to zalida shimfidaddiyar kuma k...

abdullahi dan. masud

........DAGA BAKIN DA BAITABA KARYA BA....... بسم الله الرحمن الرحيم Dasunan Allah mai rahama mai jinkai... عن عبدالله بن مسعود قال. Ankarbo daga Abdullahi dan masaud yace... "سالت رسوالله صلى الله عليه وسلم اي العمل أفضل؟ An tambabayi MANZON ALLAH S.A.W cewa menene mafificin aiki? قال: Sai yace "الصلاة لوقتها. Yin sallah a cikin lokacinta... قال قلت ثم أي؟ Sai aka ce sai kuma mi?.. .قال، sai yace...برالوالدين. Bin iyaye...قال قلت ثم أي؟ Sai aka ce sai kuma mi? قال. Sai yace..الجهادفي سبيل الله: Yin jahadi domin ALLAH Allah ka bamu ikon aikatasu

nasaba

YAYA NASABAR ANNABI (S.A.W) TAKE ??? Sunan mahaifin Annabi (s.a.w) Abdullah dan Abdul Mudallabi, sunan Abdul mudallabi (shaibah) dan Hashim, sunan hashim Amru, dan Abdul Manaf, har zuwa kakansa na 20 Adnan. Tsakanin Adnan zuwa Annabi Isma'ila dan Annabi Ibrahim, har zuwa Annabi Nuhu, zuwa Annabi Adam, wasu malaman tarihi sun kawo sunayen su duka har zuwa Annabi Adam, amma abin dayafi inganci da tabbata shine zuwa kan Adnan. Amma an tabbatar cewa duk wadanda suke cikin nasabar Annabi (s.a.w) nagartattun mutane ne masu mutunci da kamewa da asali. Mahaifiyarsa sunanta Amina yar wahbi, daga banu zuhrata, sun hadu da mahaifinsa a nasaba ta wajen kakansa kilab dan murrata, shi Annabi (s.a.w) shi kadai ne a wajen mahaifinsa da mahaifiyarsa. Ya Allah kaqara tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w).

wayapi sakarci

Cikin wayannan mutane 3 waye yafi sakarci???. 1. Wanda ake ruwan sama kamar da bakin qwarya amma ya kunna famfo yasa tiyo yana bawa flower ruwa. 2. Wanda yana jan ruwa a rijiya gugan ya fada, sai ya shiga cikin rijiyar ya laluba yaji wurin da gugan yake sannan ya fito yaje aron zabarin da zai fiddo gugan. 3. Wanda yaje daji diban giginya saida yahau bishiyan ya latsa yaji wadda ta nuna amma sai ya sauko ya riqa jifanta da dutse. Wai cikinsu wa yafi wani

Gaskiya Ne

Hakika"mafi girman haske ilimi,mafi girman duhu jahilci, mafi girman kyauta afuwa,mafi kyawun zance gaskiya,mafi munin zance karya,mafi kusantowar Al'amari tashin qiyama,mafi girman arziki wadatar zuci, mafi kyawun hali kunya,mafi munin hali kisan kai,mafi kusantar ga Allah ibada,mafi kusanci ga shaidan hasada, mafi kusanci ga Aljanna ciyarwa, mafi kusanci ga wuta rowa. Allah yadatar da mu!!!

wayo yau ina zansa kaina ne

Inason na aure Aisha,amma kuma munyi alqawari da hafsat,ita kuma maryam mun shaqu da ita,zainab kuma har gidan mu tazo jiya,ita kuma maimuna kullum sai takirani a waya, ga husna kuma jiya har kuka tayi dan wani ya zageni, ita kuma fatima ta gudu daga gidan su sbd za'a aura mata wani ba niba, khadija kuma bata da lafiya saboda jiya bata ganni ba, ko dayake bilkisuma fa tana qaunata, ita kuma amira jiya wasiqa ta aiko min da ita, zalihat kuma ina sonta,ita kuma nabila kunyarta nakeji, sai dai kuma ban kyautawa sadiya ba, amina kuma tace idan baniba sai rijiya, ko dayake mun shaqu da nafisat, fadila kuma batada lafiya sbd tsananin soyayyata, humaira kina raina, kai na tino da walida, sorry jidda, ban manta dakeba ummy, i love you ruqayya. Hmm kubani shawara dan Allah wacce zan dauka? Nasan akwai masoyana anan

ido daya gareta

A wani lokaci da ya wuce an yi wani yaro mai suna Audu, ya tsani mahaifiyarsa saboda tana da ido daya. Kuma yana ganin abin kunya ne a gare shi. Mahaifiyar tasa tana dafa abinci ne a makarantar da Audu yake. Wata rana yana aji tare da abokansa sai mahaifiyarsa ta biya ajinsa don ta duba yadda yake gudanar da karatunsa. Da ganinta, sai Audu ya bata ransa sosai, sai ya fita waje da gudu. Washe gari da ya dawo makaranta sai abokansa da suke aji daya suka fara zolayarsa, wai mahaifiyarsa tana da ido daya. Sai ranshi ya baci kuma ya ji kamar a ce ma mahaifiyar tasa ta mutu. Wata rana sai ya same ta ya ce mata “kina janyo min abin kunya da kuma abin dariya a cikin abokaina, ina ma a ce da kin mutu.” Ta yi kamar ba ta ji shi ba. Ya bi ya kosa a kan ranar da zai bar gidansu. Don haka, sai ya dage da karatu har ya samu kyautar gurbin karatu a Turai. Bayan ya girma, sai ya yi aure, ya sayi gida. Allah Ya ba shi ’ya’ya maza da mata. Wata rana yana cikin nishadi da walwala a cikin ’ya’yansa sai ma...

wani bakabe

Wani Bakabe ne ya kawo wa matarsa cefane babu magi sai ya ce mata: “Ki karbi magi a wurin makwabcinmu mai shago. Koda dare ya yi ya dawo daga aiki sai ya ce a kawo masa abinci, sai aka kawo masa danyen abinci. Ya ce: “Yaya haka?” Sai ta ce: “Ba magi.” Sai ya tashi tsaye ya ce mata: “Bari in je in sayo.” Da ya fita bai dawo ba sai bayan makonni uku. Ya da wo da asuba dauke da magi katon guda. Matar ta ce: “Maigida ina ka shiga?” Ya ce: “Magin ne ya yi wahala.” Can kuma sai ya ce mata: “Ke na manta kayana a mota.” Sai ta rike shi, ta ce: “Ai wallahi kafarka kafata, duk inda za ka.”

wani barawo ya bayarda lambar waya kafin yayi sata

Wani barawo a bihar ta kasar Indiya, ya bayar da lambar wayarsa ga wani babban jami’in gwamnati kafin ya shiga gidansa ya yi masa sata. Al’amarin ya auku a makon da ya wuce ne lokacin da barawo ya ziyarci gidan jami’in hukumar, inda ya nuna masa cewa shi limamin addinin Hindu ne, kuma mabiyin Guru Sai Baba na Shirdi. A lokacin da suke tattaunawa da bakon sai ya ba shi lambar wayarsa, ya kuma bukace shi da ya ziyarci dakin ibadarsa da ke Shirdi, inda ya ce nan ne mzauninsa. Da jami’in gwamnatinn ya ji dadin mu’amala da jabun limamin addini, sai ya shirya musu kalaci, inda daga bisani bakonsa ya bukaci ruwan sha. Da shigarsa dakin girki, don debo ruwa, sai bakon ya yi hanzari, ya kwashe sarkokin zinari da ke kan teburin dakinsa, sannan ya arce. Kayan da aka sata sun hada da sarkar zinari da zobba da zobba biyu na azurfa. Nan da nan wannan jami’in gwamnati ya tuntubi barawon ta wayar salularsa game da satar da aka yi masa. A lokacin da suke tattaunawa, wanda ake zargi da wannan sata, ya t...

zaman. duniya

Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma mun lalubo maku wasu kananan labaru ne na hikima, wadanda ke cike da hikima da koya darussan da suka shafi rayuwar yau da kullum. Muna fatan za su zama masu haska mana rayuwa, domin dai mu samu natsuwa da kwanciyar hankalin fuskantar wannan kalubale da ke ta kawo mana karo a kullum, wato kalubalen rayuwar yau da kullum ke nan. Ba tare da bata lokaci ba, za mu fara da wannan labarin: Wata rana ne wasu ma’aikata suka fito domin zuwa wurin aiki, bayan sun dauki dan lokaci sun shakata a waje. Cikin ma’aikatan akwai manajan ma’aikatar da sakatarensa da kuma daya daga cikin kananan ma’aikata. Suna tsakar tafiya sai suka ci karo da wata laya, wacce ke yashe a kasa. Ashe wannan laya ta aljanu ce. daya daga cikinsu ya sanya hannu da nufin kawar da ita daga kan hanya, sai ga wani aljani ya bayyana a gabansu. Har sun ji tsoro za su ruga, sai ya tsayar da su. “Kada ku ruga, ba zan cutar da ku ba.” Inji wannan aljani da ya fito cikin siffar mutane. “Ni aljani ...