tabayar azumi

FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN. TAMBAYA TA : MENENE I'ITIKAFI? AMSA: Ma'anar I'itikafi a larabce shine lazimtar wani abu, da tsare kai. Amma ma'anar a Shari'a shine, lazimtar masallaci ga mutunin da ya kebance kansa, a wata siffa kebantacciya da nufin ibada. I'itikafi ya tabbata a cikin littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) da kuma Ijma'in malamai. Sobada haka sai a himmatu da yinsa sosai da sosai. TAMBAYA TA : A INA AKE YIN I'ITIKAFI? AMSA: Anayin I'itikafi ne a cikin masallatai, amma ba'ayi a musalla ko a gida . Dalilinmu kuwa shine nassin Al-kur'ani ya tabbatar da haka acikin fadin sa Allah ta'ala cewa,"KUMA KADA KU KUSANCE SU (MATANKU) ALHALI KUNA I'ITIKAFI A MASALLATAI……50." Kuma Imamul Bukhari ya bude babi a cikin sahihinsa cewa: 'Anayin i'itikafi ne a Masallatai baki daya', sai ya kafa hujja da ayar da ta gabata. Hafiz Ibn Hajar ya fada acikin Fatahul Bari cewa: Mafi yawan malamai sun shardanta yin i'itikafi ne a dukkan Masallatai baki daya. Shi kuwa Imam Shafi'i cewa yayi wanda duk sallar juma'a ta zama wajibi akansa an fi so yayi shi a cikin masallacin Juma'a. Amma Imam Maliku yana ganin wajibi ne ga wanda Juma'ar ta wajabta a kansa ya yi i'itikafinsa a masallacin Juma'a. Wannan kuwa shine ra'ayin wasu manyan malamai daga cikin magabata, kamar Imam ZUHRI da sauransu…51. Amma Huzaifah Ibn Yaman (Radhiyallahu Anhu) ya ce : ' Ba'ayin i'itikafi sai a masallatai guda uku 52.' Wannan shine dalilin Shaikh Nasiruddeen Albani akan cewa ba'ayin i'itikafi sai a massalatai guda uku: Masallacin Ka'aba da Masallacin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) da Masallacin Kudus. Shi kuwa Ada'u cewa yayi: ba'ayin i'itikafi sai a Masallacin Makkah da na Madinah. Sa'idu Ibn Musayyib ya ce: Ba'ayin i'itikafi sai a masallacin Madinah kadai 53. Amma Shaikh Albani ya raunana maganar sa acikin Silsilah al-Sahihah, a karkashin Hadisin daya gabata na Huzaifah. Sai dai kuma wadansu magabata daga cikin sahabbai sun ce: Huzaifah yayi wahami ne. Daga cikinsu akwai Abdullahi Ibn Mas'ud (Radhiyallahu Anhu) domin Huzaifah yaga almajirin ibn Mas'ud suna i'itikafi a tsakanin gidan Abdullahi Ibn Mas'ud da Abu Musa al-Ash'ari, sai ya ce: Shin baza ka hana su ba? Hakik ka san Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) ya ce: "Ba'ayin i'itikafi sai a masallatai guda uku" Sai Abdullahi In Mas'ud ya ce: watakila kai ka manta, su kuma sun kiyaye, ko kuma kai kayi kuskure, su kuma sun yi daidai 54. Bayan wannan ma an samu Sa'idu Ibn Jubair da Abu Kilaba suna yin i'itikafi a masallatan unguwanninsu 55. An san Ibn Mas'ud da bin Sunnah, amma tare da haka, bai gamsu da abinda da Huzaifah yz fada ba, saboda yana da wanj ilimi da ya sabawa abinda Huzaifah ya fada. Gashi kuma Huzaifah bai ja da shi ba shiru yayi, a lokacin da Ibn Mas'ud ya ce : lailai ko dai ka manta ko kuma kayi kuskure ne. Mafi yawan makamai sun raunana Hadisin Huzaifah. Kuma ko da yake Shaikh Albani ya tabbatar da ingancinsa bisa la'akari da hanyoyinsa gaba daya, wadansu malamai na ganin cewa yin i'itikafi a Masallacin Makkah da Madinah da Kudus mustahabbi ne kawai. A bisa la'akari da wadannan dalilai da suka gabata, duk wanda ke ganin cewa, Huzaifah yayi wahami, kamar yadda Ibn Mas'ud (Radhiyallahu Anhu) ya nuna, to zai iya yin i'itikafi a kowanne masallaci, ba tare da wata togaciya ba, haka kuma, duk wanda ke ganin Huzaifah (Radhiyallahu Anhu) bai yi wahami ba, kuma hadisan sa sun inganta sai yayi i'itikafinsa a masallatan guda uku. Saboda haka muna jawo hankalin daliban ilimi musamman wadanda suke ta jayayya ko ma kafirta juna akan wannan mas'ala da su ji tsoron Allah ta'ala su san cewa wannan mas'ala ce ta ilimi, wadda magabata suka yi sabani acikinta. @Littafin: Shaikh Abdulwahhab Abdullah (Imam Ahlus sunnah wal jama'ah). *NB*** 50. Suratul Bakara aya ta (187). 51. Fatahul Bari juzu'i na hudu, shafi na (318-319). 52. Shaikh Albani ya inganta shi a cikin Silsilah Sahihah, Mujalladi na (6), kismi na farko, shafi na (667-676) karkashin Hadisi na (2786). 53. Fatahul Bari, juzu"i na hudu shafi na (319). 54. Al-Mukni'i wa sharh al-kabir wa ma'ahuma al-Insaf. Na Ibn Kudama al-Makdisi (7/577). 55. Al-Mukna'i (7/576). Sai mun sake saduwa a karo na gaba da amincewar Allah.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA