BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)
BISMILLAHIR RAHAMANUR RAHIM
WASSALALLAHU ALANNABIYUL KHARIM
NASIHA GA MATA A KAN JININ HAILA.
HAILA:- (Jinin Al’ada na mata)
Jinni ne wanda da kansa yake fitowa daga FARJIN mace wadda a al’ada Zata Iya Daukar Ciki.
SHEKARUN DA MATA SUKE YIN AL’ADA
Daga shekara tara (9) zuwa goma sha uku (13) in dai jini ya fitowa mace to na al’ada ne ma’ana ta fara al’ada kenan, wato zata iya daukar ciki kenan.
LOKACIN DA YAKAMATA A LURA DA SU WAJEN ZUWA DA DAUKEAWAR JININ HAILA.
Sune: Daukewar (HAILA (Jinin Al’ada)
1. KAFIN FADUWAR RANA
Idan jinin al’ada ya dauke lokacin da mace zata iya yin sallah raka’a “5” kafin rana ta fadi (wato zata sami yin “AZAHAR” raka’a hudu kuma ta yi raka’a “1” daya sallar “LA’ASAR” sannan rana ta fadi). A wannan lokacin dole ne tayi sallar AZAHAR da LA’ASAR na wannan rana.
Idan jinin Al’ada ya dauke lokacin da mace zata iya yin sallah raka’a hudu (4) kafin ALFIJIR ya keto dole ne tayi sallar MAGARIBA data ISHA’I na wannan rana.
Idan kuwa jinin Al’ada ya dauke lokacin da mace zata iya yin sallah raka’a uku (3) kafin hudowar alfijir zatayi sallah ta ISHA’I kadai banda sallar MAGARIBA.
ZUWAN JININ HAILA (JININ AL’ADA).
2. FADUWAR RANA:
i. Idan jinni ya zowa mace a daidai lokacin da zata iya yin sallah raka’a biyar “5” kafin rana ta fadi alhali ba tayi sallar AZAHAR da LA’ASAR ba to a nan bayan daukewar jinin bazata rama sub a.
ii. Idan jinin ya zowa mace lokacin da zata iya yin sallah raka’a hudu (4) kafin faduwar rana alhali ba tayi AZAHAR da LA’ASAR ba to a nan bayan daukewar jinin zata rama sallar AZAHAR don a Lokacin sallar LA’ASAR ya zo mata.
3. FITOWAR ALFIJIR
i. Idan jin ya zowa mace lokacin da zata iya yin sallah raka’a hudu (4) kafin hudowar alfijir, alhali bata yi sallar MAGARIBA da ISHA’I ba to bazata rama MAGARIBA da ISHA’I ba bayan daukewar jinni.
ii. Idan jinni ya zowa mace lokacin da zata iya sallah raka’a uku (3) kafin hodowar alfijir bata yi sallar MAGARIBA da ISHA’I ba to anan zata rama sallar MAGARIBA bayan daukewar jinn.
ABIN LURAR SHINE
Da yawa wasu yadda suka dauka idan mace kwana uku (3) takeyin haila wato (jinin al’ada) idan ya kwana uku (3) bai daukeba sai akara kwana uku (3) idan bai daukeba sai ta kara kwana uku (3) tayi tayin haka har kwana goma shabiyar (15) kuma duk a wata daya (1) toba haka ba ne wannan kuskure ne yadda yake shine kamar yada mukayi bayani daki-daki a baya.
MISALI:
Idan kwana hudu (4) kike yin al’adarki a watan yazo kika ga bai tsayaba to kwana uku (3) zaki kara in ya tsaya shi kenan in bai tsaya ba to ya zama jinin cuta sai ayi wanka a ci gaba da ibada. Haka in wani watan yazo shima bai tsaya ba to kwana uku (3) dai zaki dada har in yazo wani wata da ya zama kwana (13) bai tsaya ba. To a nan kwana biyu (2) zaki kara ya zama kwana (15) in ya tsaya shike nan in bai tsaya ba to, sai kiyi wanka ya zama jinin cuta.
Haka in kwana (5) ki keyi wani watan dayazo bai tsayaba, ki kara kwana (3) har watan da yazo ki kara (3) wani watan da yazo kika kara kwana uku (3) ya zama (14), to in wata gaba yazo bai tsaya ba to kije kiyi wanka yazama na cuta duk Karin da zakiyi bazai wuce kwana goma shabiyar (15) ba.
MARAR KWANA TSAYAYYU
Idan ya zama baki da kwanaki tsayayyu.
MISALI:
Wannan watan in ki kayi kwana (3)wani watan ya zama kwana (4) wani watan ya iya zuwa biyar (5) to saiki duba a wanne ne yafi yawan kwanaki ga (3) ne, ko ga hudu (4)ne, ko dai ga biyar (5) ne.
To sai kikaga na kwana biyar (5) yafi yawa to duk ranar da kika ga kin zo yin al’ada kika ga kikai kwan biyar (5) jinni bai tsaya ba to daga kwana biyar (5) zaki fara kirgenki. Kari kuma sai ki kara kwana uku (3) kinga yakai takwas kenan.
ALAMAR DAUKEWAR JINNI HAILA (AL’ADA)
Alamar samun tsarki guda biyu (2) ne akwai kekasar auduga akwai kuma farar kassa.
1. Idan kika jawo wannan audugar da kike kuzugu da ita, bayan da kin jawota kika ganta bushashiya babu wani danshi na jinni a jikinta, to wannan alama ce ta kin sami tsarki.
2. Idan kuma kika jawo audugar kika ga wani irin farin ruwa-ruwa wato (farar kassa) a jikin wannan audugar to wannan ya nuna kin sami tsarki saboda haka sai kije kiyi wanka.
WANKA
Abubuwan da suke wajabta wanka a muslunci suna da yawa wasu daga cikinsu sune:
JANABA, DA DAUKEWAR JININ HAILA DA BIKI.
Ita janaba tana samuwa ne ta hanayar fitar da mani a bacci ko a farke, ta hanyar jin dadi wanda aka saba ga namiji ne manin ya fito ko mace babu banbanci.
Haka nan janaba tana samuwa ne ta hanyar hada farjin mace da namiji ko mani ya fito ko bai fito ba. Haka janaba tana samuwa ta hanyar boye hashafa (kan gaban na miji inda akyi masa kaciya) a cikin wata kafa ta wani abu mai rai, mutum ne ko dabba.
DAUKEWAR JININ HAILA DANA BIKI
Idan jinin haila ya daukewa mace ko na biki to sai tayi wanka.
YANDA AKE WANKA IBADA A MUSULUNCI.
i. Ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa
ii. Wanke hanun dama dana hagu zuwa tsintsiyar hannu sau uku (3).
iii. Wanke duk inda wata najasa take a jiki.
iv. Za’a wanke gabobin alwala sau dai-dai tun daga hannu har izuwa kafa.
v. Sai ya wanke hannunsa da ruwa ya shafe tafikan hannayensa da ruwa ya kwara a kansa. Ya wanke ya caccuda ya mur-murza gashin kansa zaiyi har sau uku (3). Idan macace itama zata kwara ruwan kamar haka ba sai ta tsefe kitson kanta ba indan da kitson kenan, sai dai idan yakasance anyishi da roba koda wani zare wanda ya rufe gashin kan baki daya, to sai an tsafe.
vi. Sai a wanke wuya, fuska da da duk abin da ta kunsa.
vii. Sai a wanke tsagin jiki na dama tun daga kafada har zuwa tafin kafarsa, haka kuma zai wanke tsagin jikinsa na hagu kamar haka.
viii. Ana so mutum mai wankan yabi dukkanin wata gaba a jikinsa wadda take da tattara ya wanketa a hankali – a hankali , misali cibiya mai zurfi sai mutum yasa dan kuri ya cuccuda yana zuba ruwa. Haka gwiwar hannu da gwiwar kafa sai ya tankwashe ta sannan ya wanke haka kuma karkashin gwiwar kafa sai an mikar da kafar sannan ya wanke, haka nan matse-matsin duwawun dama dana hagu shima a wanke hankali, haka idan mutum yana da kunshi ko faso sai ya mai da hankali wajen wankewa a hankali yana wankewa har sai wajen ya wanku, haka kuma anso ya zuba ruwa a tafinsa na hagu sai ya sa kan “yan yatsunsa na hagu ya girgiza.
Wannan itace hanyar da akebi wajen yin wakan haila ko na biki ko na janaba.
ALHMDULILLAHI RABBIL ALAMIN.
Mungode ALLAH ya saka
ReplyDelete