maanar azumi
MENENE MA'ANAR AZUMI? Ans: Ma'anarsa a shari'a shine kamewa daga dukkan abubuwan da suke 6ata azumi,kamar ci da sha da Jima'i da sauransu, daga ketowar Alfijir zuwa faduwar Rana da niyyar bautawa Allah. MENENE DALILIN WAJIBCIN AZUMI? Ans: Dalilin wajibcin azumi shine fadar Allah madaukakin sarki "Ya ku wadanda kukayi Imani an wajabta muku yin Azumi kamar yadda aka wajabta wa wadanda suka gaba ceku ko kunji tsoron Allah". Kwanakine Kididdigaggu. Kuma hadisi ya ingata daga Abu huraira RA. Manzon Allah s.a.w. Yace " kuyi Azumi idan kun ganshi"........ Wannan kuwa umurni ne. Ana Iya daukar azumin koda mutum dayane yaga wata domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi dan Umar R.A yace "mutane sun rigeni ganin jinjirin wata saina gayawa manzon Allah s.a.w sai yace" suyi azumi". Duba Abu Dauda 2340, Hakim da Ibn Hibban suka inganta shi: Hakim 423. Ibn Hibban 3438. Amma mafi yawan malamai sunce ganin mutum daya ga watan to lallaine yazamto Adali watau wanda ba zaiyi qarya ba
Comments
Post a Comment