wata rana

" Wata rana wani mutum yazo wajen Wani Malami domin ya warware masa matsarlar cikin gidansa. Yace, Malam inada matata mun dade tare, kuma muna da yara, amma yanzu sam bana jin sonta da sha'awarta a cikin zuciyata. Sai Malami yace, mai yasa baka sonta ?Ta canja fasali ne ko tayi kiba dayawa ?Sai mutumin yace a'a, tana nan kamar yadda take kafin in aureta. Malami ya sake cewa ko kuma tasamu nakasa a dalilin wani hatsari? Yace ko daya Malam.. Can sai Malamin nan yace dashi. Hakika zuciyarka ta karfafa wajen kallon matan waje da suke wucewa,sannan kuma kana shagalta da kallon hotunan batsa. Nan da nan mutumin mamaki ya kamashi. Ya sunkuyar da kai, yace Malam wannan zance haka yake. Amma yaya akayi kagane hakan tattare dani? Sai Malamin yace: "Idan har zuciyarka ta dulmiya zuwa ga Haram, ko kana cin Haram, ko kana mu'amala da abubuwan Haraam, ko shakka babu zaka zama mai gujewa "HALAL". Ya Allah ka kiyaye zukatanmu daga aikata alfasha.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA