Niyyar yin jima'i

NIYYAR GABATAR DA JIMA'I

Sahabin manzon Allah (s.a.w) ya fada a cikin wasiyyarsa cewa.

"A lokacin gabatar da jima'i, ya kamata ango ya daura wadannan niyyoyi."

1. Ango ya daura niyyar Kare kansa daga zina.

2. Da niyyar kare kansa daga kallon matan da ba halal din sa ba.

3. Da niyyar samar da "ya"ya na gari wadanda zasu yiwa Musulunci hidima.

Idan har ango ya gabatar da jima'i da amaryarsa tare da kyakkyawar niyya ya sami gamsuwa da ita akwai lada da Allah madaukakin sarki zai bashi wannan na nuni ne da muhinmmancin sanya kyakkyawar niyya a zukata kafin saduwar jima'i, kuma ana samun falala daga wannan niyyoyi kyawawa, an so a lokacin da ango da amarya ke shirin saduwa da juna su ta6e tufafinsu sannan su lullu6a, su kashe fitila, kamar yadda aka samo cikin wani hadisi, Jabir bin Abdullahi, Allah ya yarda dashi yace; Manzo (s.a.w) yace idan duhun dare ya gabato ko kuma almuru tayi to ku hana "ya"yanku fita.

Domin shaidanu suna bazuwa a wannan lokaci. Idan sa'a ta gota a cikin dare, to sai ku bar su. Ku rufe kofofi, kuma ku ambaci sunan Allah (yayin da ku ke rufewa) domin shaidan baya bude kofa fufaffiya.

Ku zage bakin salkunan ruwanku, kuma ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke rufewa) ko da ku dora wani abu ne a kan kwanika kuma ku kashe fitilunku.

Allah ya yi dadin tsira da aminci da albarka ga Annabinmu Muhammad da alayansa, da sahabban

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA