assalamualaikum
Assalamu alaikum warahmatullah, Yan uwa barkanmu da saduwa a wannan littafi mai albarka na Umdatul-Ahkam, a darasin daya gabata mun tsayane a hadisi na 63 a BABIN FALALAR SALLAR JAM'I, ayau kuma da yardan Allah zamu ci gaba: 64. An karbo daga Abu-Hurairah R.A yace: Manzon Allah s.a.w yace: Mafi Nauyin Sallah ga Munafuqai itace: Sallar ishaa'I da Alfijr, Da ace sunsan abin dake cikinsu (na falala) da sunjesu koda da jan ciki ne, haqiqa na himmantu akan na Umarcesu da sallah, sai a tayar da ita, sannan na Umarci mutum, yayi sallah tareda Mutane, sannan na tafi da wasu daga cikin mazaje, tare dasu su daukamin itatuwa, mutafi ga mutanen da basu halartan sallah, sai in qone gidajensu da wuta. 65. An karbo daga Abdullahi bn Umar R.A, Daga Manzon Allah S.A.W yace: Idan Maatar dayanku tanemi izininsa zuwa masallaci, to kada ya hanata. Ya ce: sai Bilaal bn Abdillaahi yace: Na rantse da Allah sai mun hanasu. Yace: sai Abdullahi (bn Umar) ya fuskance ya zageshi zaagi mai tsanani, ban taba jin yayi irin wannan zaginba tunda nake, sannan yace: Tayaya ina baka labari gameda Manzon Allah s.a.w sannan kai kanacewa: Wallahi sai mun hanasu?? FAA'IDAH: Sallolinda sukafi yiwa munafuqai wuyar yi a Jam'I sune: Ishaa'I da Asubaahi, domin kuwa ana sallar Ishaa'I ne bayan an dawo daga harkoki, sannan anci abinci ana hutawa! Ita kuwa asubaahi, lokacin ana cikin jin dadin barcine, hakan na sanya sai mai qarfin Imanine kadai zai iya tashi yaje yayi wadannan sallolin, munafuqi kuma baya iya zuwa yinsu a jam'I, domin Annabi ya nuna mana muhimmancin wadannan sallolin, yace: INDA MUTUM YASAN FALALAR SU, DA KODA JAN CIKINSA NE SAI YAJE! Sannan Annabi S.A.W yana qara nuna mana illar qin yin wadannan sallolin A Jam'I, yake cewa: Naso in Umar ci mutane suyi sallah, maimakon nayi musu limanci, sai nasanya wani daga Musulmi yayi musu, ni kuma na dibi wasu mazaje, mu tafi da itatuwa, muna bi gida gida, duk gidan da muka samu masu shi suna ciki basu tafi sallah ba, sai mu cinna masa wuta, muqoneshi suna ciki, duk su qone baki daya. Bayani gameda hadisi na 2 kuma sai a darasi na gaba, domin bayanine mai tsayi, wanda Malamai sunyi maganganu masu yawa akai! Don haka yana da kyau mu tsaya mu warware bayanan, domin kaudafitina! Wallahu A'alam. Ubangiji Allah yasa mu gyara kurakuran mu. Nidai nace ameeeen. saura ku/ _________________________
Comments
Post a Comment