gaskiya mai daci
GASKIYA MAI DACHI ********************* Yawancin Mutane sun dauki Azumi amatsayin wani lokaci ne wanda ake wuni da yunwa.. Don haka akwai Bukatar gyara abinci sosai domin idan lokacin shan ruwa (buda-baki) yayi, Kaci da yawa sai ka Qoshi. Don haka zaka ga wasu Har time-table sukeyi na Kala-kalan abincin da zasu rika yi akullum. Yawancin mutane suna Mantawa da BABBAN ABINDA YAFI MUHIMMANCI shine ka samu Tsoron Allah. Ta hanyar wuni da yunwa, so ake ka tuna da cewa akwai fa wasu bayin Allah wadanda ko yaushe cikin kwanakin shekara ahaka suke wuni, ahaka suke kwana!!! Ida ka dandana irin halin da suke ciki, to kaga kenan zaka fi jin tausayinsu da kokarin taimaka musu akoda yaushe. Abu mafi muhimmanci shine kaji acikin zuciyarka cewa ibada kakeyi, ka taimaka ma Makobtanka da 'yan uwanka, kuma ka samu Tsoron Allah azuciyarka. Time table na Ibadar nafilfili da Karatun Alqur'ani yafi Muhimmanci fiye da Timetable na abincin da zaka rika ci. Da yawa wasu basu da wata riba acikin yin Azuminsu sai dai yunwa, Kuma da yawa wasu basu da riba cikin Tsayuwar darensu sai dai rashin barcin.. Ya Allah ka kiyaye mana imaninmu, ka Qara mana Taqawa da Son Manzonka (saww).
Comments
Post a Comment