ido daya gareta
A wani lokaci da ya wuce an yi wani yaro mai suna Audu, ya tsani mahaifiyarsa saboda tana da ido daya. Kuma yana ganin abin kunya ne a gare shi. Mahaifiyar tasa tana dafa abinci ne a makarantar da Audu yake. Wata rana yana aji tare da abokansa sai mahaifiyarsa ta biya ajinsa don ta duba yadda yake gudanar da karatunsa. Da ganinta, sai Audu ya bata ransa sosai, sai ya fita waje da gudu. Washe gari da ya dawo makaranta sai abokansa da suke aji daya suka fara zolayarsa, wai mahaifiyarsa tana da ido daya. Sai ranshi ya baci kuma ya ji kamar a ce ma mahaifiyar tasa ta mutu. Wata rana sai ya same ta ya ce mata “kina janyo min abin kunya da kuma abin dariya a cikin abokaina, ina ma a ce da kin mutu.” Ta yi kamar ba ta ji shi ba. Ya bi ya kosa a kan ranar da zai bar gidansu. Don haka, sai ya dage da karatu har ya samu kyautar gurbin karatu a Turai. Bayan ya girma, sai ya yi aure, ya sayi gida. Allah Ya ba shi ’ya’ya maza da mata. Wata rana yana cikin nishadi da walwala a cikin ’ya’yansa sai mahaifiyarsa ta kawo masa ziyara. Ta ce masa ta jima ba ta gan shi ba da kuma jikokinta shi ne ya sa ta zo. Daga ganinta sai ’ya’yansa suka fara dariya, wasunsu kuma suka fashe da kuka wai ta zama abin tsoro. Nan take Audu ya ce mata “ya za a yi ki zo ki tsoratar min da ’ya’yana? Maza! Ki fita min a gida.” Sai ta ba shi hakuri ta ce ashe ta yi batan hanya ne, sai ta bar gidan. Wata rana sai ya sami wasika daga makarantarsa inda mahaifiyarsa take aiki a kan cewa tsofaffin dalibai su zo a yi shawara kan ci gaban makarantar. Sai ya yi wa matarsa karya ya ce wai zai yi tafiya a kan al’amuran kasuwancinsa. Bayan ya isa makarantar kuma an gama shawarwari, sai ya biya gidan mahaifiyarsa don ya yi mata gargadi game da zuwan da ta yi ba tare da ya gayyace ta ba. Da ganinsa makwabtansu sai suka gaya masa ai ta mahaifiyarsa ta rasu, kuma suka mika masa wata wasika kamar haka: Zuwa ga dana abin alfaharina, Kullum ina cikin tunaninka. Don Allah ka yafe ni da na je gidanka ba tare da ka gayyace ni ba, kuma na tsoratar maka da ’ya’ya. Da na ji an ce za a kira tsofaffin dalibai su zo su yi shawara kan ci gaban makarantan nan, na yi farin ciki, kuma ba don komai ba sai don damar da zan samu in ganka. Ga shi kuma ba zan iya ganin ka ba don ina kwance a gado, kuma ciwo ya matsa min, don haka ka yafe min da na zama abin kunya a gare ka lokacin da kake yaro. A lokacin da kake yaro, ka hadu da hadari wanda ya sa ka rasa idonka daya, a matsayina ta mahaifiyarka, ba zan iya ganin ka har ka girma da ido daya ba, shi ne na sa likita ya cire nawa ya ba ka. Kuma kullum na ganka da idanunka kamar na sauran jama’a, sai farin ciki ya kama ni. Ni ce mahaifiyarka. Bayan ya gama karanta wasikar sai ya fashe da kuka, ga shi kuma babu halin ya roke ta gafara don ta rasu, hakan ya sanya kullum yana cikin bakin ciki da kuncin rayuwa.
Comments
Post a Comment