bani isra'il

Anyi wani Mutum mai sabon Allah a cikin Bani Isra'ila, iyalan shi suka fadakar da shi a kan ya daina sabon Allah amma bai fadaka ba. Sai Allah yayi wahayi zuwaga Annabi Musa(alaihi ssalaam) bisa cewa: ya fitar da wannan mai sabon Allah kada azaba ta same su. Sai wannan Mai sabo ya bar wannan gari zuwa wani. Sai Allah ya umarci Annabi Musa (alaihis salaam) da ya je ya fitar da shi daga wannan gari. Sai wannan mutum ya tafi wani kogon dutse ya tare a ciki yana mai tuba zuwaga Allah. Sai Mutuwa tazo ma wannan mutum, sai yake cewa: Wayyo Allah! Da Mahaifiyata tana kusa da ta taimaka mani, kuma da tayi mani kuka saboda halin da nake a ciki. Wayyo Allah da Mata ta tana kusa da tayi mani kuka saboda halin da make ciki, haka yaya na da. Wayyo Allah da Babana yana kusa da yayi mani wanka! Ya Allah! Kamar yadda ka yanke tsakanina da iyali na, kada ka yanke ni daga rahamar ka. Ya Ubangiji kada ka kona ni da wutar ka saboda sabo na. Nan take sai Allah ya turo Hurul'ini a cikin surar Mahaifiyar shi, kuma ya turo wata Hurul'ini a siffar Matar shi, kuma ya turo Mala'ika a surar Mahaifin shi, sannan ya turo wasu yaran Aljanna a surar yayan shi. Lokacin da ya gansu sai ran shi yayi mashi dadi. Kuma sai Allah ya sake yin wahayi ga Annabi Musa(alaihis salaam) cewa: ka tafi zuwa ga Waliyyi a waje kaza, kayi mashi wanka. Lokacin da Annabi Musa ya ganshi, nan take ya gane fa wannan mutumin ne mai sabo. Sai yace: ya Allah menene yasa ka gafarta mashi? Sai Allah yace: Saboda rabuwar shi da iyalin shi da garin shi. Domin Bako idan ya mutu Mala'ikun sama da kassai da sammai suna yi mashi kuka. Don menene ni ba zan gafarta mashi ba, gashi nine mafi jin kan masu jin kai. Ya Allah ka jikan mu, ka gafarta mana, ka kyautata makwancin mu idan mutuwar mu ta zo.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA