falalar Azumi

FALALA ASHIRIN (20) TA WATAN RAMADAN 1, A cikin sa aka saukar da Alkurani mai girma, Bakara 185 2, Dukkan littafan Allah mai girma, a cikin sa aka saukar da su, takardun Annabi Ibrahim a daran farko na watan, Attaurar Annabi Musa a ranar 6 ga watan, Injilar Annabi Isa 13 ga watan, Alkur'anin Annabi Muhammad saw, a ranar 24 ga watan, Musnad Ahmad, shaik Albaniy ya ingantashi. 3, Ana bude Kofofin Aljannah a cikin watan, 4, Ana rufe kofofin wuta 5, Ana daure kangararrun shedanu 6, Ana bude kofofin Rahma 7, Ana bude kofofin sama 8, mai kira yana kira, ya mai neman alkhairi gabato, ya mai neman sharri, kayi nisa 9, A ko wanne dare, Allah yana yanta bayi daga wuta 10, A cikin watan akwai daran lailatul kadri wanda yafi wata dubu, 11, Ana kankare zunubin shekara, Annabi saw yace, Daga Ramadana Zuwa Ramadan aka kankare zanubi duka, mutukar an nisaci kaba'ira 12, An durmuza hancin, Duk wanda Ramadana ya kama har ya wuce baiyi aikin da zaayi masa Rahma ba. 13, Umra a cikin watan Ramadan daidai yake da aikin hajji tare da Annabi, saw a wajan lada. 14, watan da akafi shiga I'itikaf, a goman karshe 15, Watan da ake amsa Addu'a 16, Watan da akeson yawaita Karatun Alkur'ani mai girma, akalla sauka hudu, duk sati daya. 17,Watan Alkhairi da kyauta da ciyarwa, da samun dumbin lada, duk wanda ya ciyar da mai azumi, zai kara samun lada kamar yayi azumi. 18, Watan da akafi yawan kiyamul laifi da tarawih da Tahujjud da Asham, don kara kusanci da Allah. 19, Watan neman nasara akan makiya, Sahabbai sukanyi amfani da watan Ramadan, wajan addua mai tsanani akan makiya. 20, watan sada zumunta,da karfafa, yan uwantaka ta musulunci, Allah ka kaimu Ramadan, da imani da son Allah da Manzonsa, Ka karbi ibadun mu ka yafe mana. Ya Hayyu Ya Qayyum.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA