hadith

↓ Sahihin Hadisi Daga Cikin SAHIHUL MUSLIM, Daga Sahabi Abu Zarril Giffari Ya Ce:- "Watarana Muna Zaune Tare Da Manzon ALLAH(S.A.W) Da Yamma, Sai Rana Ta Tafi Zata Fadi Sai ANNABI(S.A.W) Ya Ce: 'Ya Abu Zarr Ko Kasan Inda Ranar Nan Zata Fadi???' Sai Abu Zarr Ya Ce: ALLAH Da Manzonsa Ne Sukafi Sani, Sai ANNABI(S.A.W) Ya Ce: Ai Ba Faduwa Takeyi Ba, Tana Zuwa Gaban ALLAH (S.W.T) Ne, Sai Ta Fadi Tayi Sujjada Ga ALLAH(S.W.T) Idan Tayi Sujjadar Sai ALLAH Ya Bata Dama Sai Ta Wuce, Shine Sai Ta Bullo Ta Gabas Idan Gari Ya Waye, To Ana Nan Watarana Zata Je Tayi Sujjada Gaban ALLAH Sai ALLAH Ya Ce:- An Karbi Sujjadarki Amma Yau Ba Za'a Baki Hanya Ba, Ki Koma Ta Inda Kika Fito, Idan Ta Koma Kuma Gari Ya Waye Sai Ta Bullo Ta Yamma...... To a Wannan Lokacin Ne Fa Da Zaran Rana Ta Bullo Ta Yamma To An Rufe Kofar Karbar Tuba Babu Wani Wanda Zai Tuba ALLAH Ya Karbi Tubansa Kuma a Wannan Rana Ne Ko Da Kafiri Ya Ce LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH (S.A.W) To ALLAH Ba Zai Karbi Wannan Shahadar Ba". Ya ALLAH! Kasa Bamu Cikin Wadanda Zaka Rufe Kofar Tuba Ba Tare Da Mun Tuba Ba. Ya Allah ka rabamu da masifun duniya da lahira, dan darajar fiyayyen halitta.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA