labarai

Jagoran Musulunci A Kasar Yarbawa Ya Rasu Rahotanni daga birnin Ibadan babban birnin jihar Oyo ya tabbatar da cewa fitaccen dan kasuwan nan kuma jagoran addinin Musulunci a jihar Abdulazeez Arisekola Alao ya rasu a jiya a wani asibiti da ke kasar Switzerland. Wata majiya daga iyalan mamacin ta bayyana cewa mamacin ya rasu ne sakamakon ciwon kansa, sannan kuma ana shirin kawo gawar Nijeriya domin yi masa jana'iza a gobe da safe kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. A shekarar 1980, wata kungiyar malaman Musulunci sun ba shi mukamin 'Aire Musulumi Of Yorubaland, ma'ana uba ga Musulman kasar kabilar Yarbawa, wanda hakan ya ba shi zama daya daga cikin masu yi wa addini hidima a yankin kasar Yarbawa. Bayan kasancewarsa hadimin addinin Musulunci a Nijeriya, marigayin hamshakin dan kasuwa ne. An haifi marigayi Alao a 1945, inda ya fara harkokin kasuwanci a matsayin dan tireda har zuwa lokacin da Allah ya nufa ya zama cikakken dan kasuwa. Sannan kuma ya rasu ya bar mata da yara da dama

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA