maye burinka cikin wata maialfarma
MEYE BURINKA/KI A WATAN AZUMI..............?????!!!! Hakika kowane dayanmu yana da Bukata ta musamman a wajen Allah. To Watan Ramadhan da kuma Azumin cikinsa ya bamu dama mai yawan gaske domin biyan Bukatar tamu. 1- Lokacin Buda Baki ana karbar Addu'ar Mai Azumi. 2-Lokacin yin Sahur ma ana Karbar Addu'ar Mai Azumi. 3- A cikin Sallah lokacin Sujjadah ana karbar Addu'a,ga kuma lokaci ne na yawaita Sallolin Nafila. 4-Lokacin da ka taimakawa Dan uwanka saboda Allah,shima lokacin karbar Addu'a ne. 5-Lokacin Sauka ko gama Karatin Qur'aani,shima lokacin Karbar Addu'a ne. Hakika ga wanda duk ya ribanci wan nan Watan,to cikin Taimakon Allah zai sami biyan Bukatunsa daga Allah Madaukakin Sarki. Muna godiya ga Allah,wallahi cikin ikon Allah dukkan Ramadhan,sai na sami kusan biyan bukatar da nasa a gaba. Allah ya karbi ibadun mu gaba daya,ya kuma kiyaye mu Azabar Wuta,ya sanya mu a Aljannah!!!
Comments
Post a Comment