koliya datsafta

KWALLIYA DA TSAFTA A CIKIN AZUMI Kwalliya da tsafta a cikin Azumi, marhaban lale azumi na hanya ya kusa saura qiris, kuma muna farin ciki da shirin zuwan sa. Wannan ne dalilin da ya sa na ga ya dace na yi magana a kan irin kwalliyar da ta dace da wannan wata mai albarka, da kuma yadda ya kamata ki tsaftace gida da jiki. Tsaftar muhalli dai kowa ya san abu ne mai kyau ga xan adam, saboda haka yana da kyau uwargida ta tsaftace muhallinta da canja duk wani abu da ki ka san ya tsufa da sabo balle ma wajen girki. In kuma babu halin canjawa sai a gyara ko ina, ko a canja musu wuri a xauke daga wurin da su ke da su koma wani sabon wurin, saboda shi zai qara wa kitchen xin da xaki kyau da martaba ban da tara tarkace, xebe shirgi da adanawa na gyara gida da canja labulaye. Ina qara jan hankalin mata kar kice ni bani da shi saboda haka ba zan gyara ba, da wanda ki ke da shi xin zaki gyara don mijinki ya ga canji, ki sani su maza ‘yan son su ringa ganin sabon abu ne don yana qara sa su ji daxi da son zaman gida saboda gidan su yana birge su. Shi wannan wata mai zuwa saboda darajarsa ya isa uwargida ta zama wata ta daban a wurin mijinta, ta canja salon gidanta da xakin girkinta da salon kwalliyar jikinta. Su kan su ‘yan mata ya kamata su canja salon shigar su da kwalliyarsu, yana da kyau shiga ta zama ta kamala da kwalliya wacce bai kamata ta xauki hankalin namiji ba. Gida da farko dai ya kasance tsaftatacce sai kuma qamshi ya biyo baya. Dogayen riguna masu kyau a wannan lokacin su suka fi kyau da irin shigar da ya dace da wannan wata ga budurwa ko matar aure. Ita kanta kwalliyar kar a ringa rambaxa kwalliya kamar za aje gidan biki, sannan kar a ringa saka turare mai qarfi ko wanda qarfinsa ke hawa kai.s

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA