mace tagari
MACE TA GARI Wata rana wani talaka cikin magavata ya tsinci jaka a kasuwa, a lokacin kuwa basu da abin da zasu ci a gidansa, dan haka ya koma gida suka bude jaka da matarsa. Suna budawa sai suka ganta cike da Dinare, sai mijin yace Allah ya taimakemu arziki har gida,! koda matar taji haka sai tayi masa nasiha akan ya koma kasuwa, ya nemi me jakar ya bashi abinsa. Koda ya dawo ya gamu da me jakar, yayi masa cikakakken bayanin da ya tabbatar masa tasace, saiya maida masa kayansa.! Koda mai jaka ya karba sai yace masa:"malam kai talakane ko mai arziki", sai talakan nan yamasa bayaninsa a takaice, sai mai kudin ya miko masa jakar da dinaran yace dama wannan zakkatace ta bana na ware zan bawa wanda ya cancanta dan haka jeka na baka. Yaa Allah ka azurta mu da mata nagari masu halin kwarai...!
Comments
Post a Comment