ILU
Mallam Ilu ne yaje wurin wa'azi sai yaji mallam yana cewa duk wanda ya kwanta da matarsa, sau daya, kuma ya samu biyan bukata da ita toh ladansa a wurin Allah kaman ya kashe arna saba'in ne. Mallam Ilu yana dawo wa gida, sai ya samu matarsa luba tana gida tana dan wanke wanke, ya kirata Luba! Tace eh yace ashe a harkan ga alheri na sosai bamu sani ba? Luba tace wace harka? Sai yabata labari abinda Mallam ya fadi a wa'azi. Sai tayi kaman bata damu ba, Masha Allah dare yayi kaman yanda Mallam yayi bayani, Mallam Ilu ya kwanta da matarsa kwanciyar sunna ya kashe arna saba'in. Ya ja bargo ya rufa, chan dare matarsa Luba tace Ilu Ilu! Yache eh mi? Tace tashi ka kashe arna, Ilu ya tashi ya kashe arna saba'in. Ilu ya ja bargo ya rufe, chan tsakiyar dare ta tashe shi Ilu! Yace mi? Yace arna koh? Tace eh arna! Ya tashi ya kashe saba'in da kyar. Chan karshen dare ta sake tashinsa Ilu! Yace mi Luba? Tace arna! ya aje bargo gefe guda yace ke Luba waye sarkin yakin manzon Allah? Tace Sayyadi Ali, yace toh ko shi ya mutu ya bar arna!
Comments
Post a Comment