wata rana
Watarana wani mutun yaje wajen wani malam, sai yace Mallam ni matashine mai tsananin sha'awa,kuma kullum ina cikin kallon mata a kasuwa,don Allah mallam ka bani shawara... Sai malam yayi shiru na dan lokaci,sai yace mishi ina zuwa. Ya shiga cikin gida ya dawo rike da kofi a hannunshi. Ashe madarar shanu cike fim a kofin kamar zai zube. Sai ya mika mishi,yace kafin in baka shawara zan aikeka, rike wannan madarar ka kaiwa wane a cikin kasuwa(ya mishi kwatancen wanda zai kaiwa).. Ya tashi zai tafi, sai malam yace amma akwai sharudda akan wannan madarar. Bana so ko digo daya ya zuba a kasa,idan kuma ya zuba,ga almajirina zaku tafi tare dashi, yana binka a baya da tsumagiya,idan yaga digo daya ya zuba a kasa zai shauda maka ita da karfinsa..Sai mutumin yace Mallam bazan barima ya zube ba! Cikin sa'a kuma sai ya kai madarar ba tare da zubar da digo ba..Ya iso ga Mallam cikin murna yace na isar da sako yadda ka umurceni. Sai Sheik yayi murmushi yace,akan hanyarka ta zuwa fuskokin mutane nawa ka gani? Sai yace Allah gafarta Mallam aini babu fuskan dana gani. Yace tunda na rike madarar ban san meke faruwa a kasuwa ba,hankalina yana kai kar ya zube a zabga min bulala a gaban 'yan kasuwa,kunyar hakan ya sameni yasa ban lura da komai ba.. Sai malam yayi murmushi,yace hakika kowanne Mumini haka yake. Kullum yana tsoron Allah,kuma yana jin kunyarsa a bainar 'yan Adam,kar ya yi sabo ko zunubi.. Wadannan sune mutanen dake kare kansu daga zunubi saboda kullum hankalinsu yana kan ranar alQiyama.. DARASI...Kullum mu kasance cikin tuna Allah,idan har shaidan zai saka aikata wani abun sabo ko zunubi,ka tuna cewa Allah Yana kallonka..Allah Ya bamu sa'a a duniya da
Comments
Post a Comment