dolle adaina shigo da janareta nigeria taron kasa

A farkon makon nan ne wakilan taron kasa da ke gudana a Babban Birnin Tarayya Abuja suka yi kiran a dakatar da shigo da injunan bayar da hasken lantarki na janareta bakidaya a kasar nan a matsayin wani kwakkwaran mataki na habaka bangaren lantarkin kasar wadda ya kasance cikin mawuyacin hali tun da dadewa. Wakilan sun yi kiran ne a sa’ilin da ake tattauna rahoton kwamitin da taron ya kafa a kwanan baya a kan makamashi. Sun bayyana cewa ci gaba da sayo injunan janaretan daga waje yana dakushe kokarin wadata kasar da ingantacciyar wutar lantarki. Daya daga cikin wakilan, Chris Abongabe ya nunar da cewa idan Nijeriya za ta sanya gawayi a cikin abubuwan da take amfani da su wajen samar da makamashi, za a samu kyakkyawan sakamako. Wakazalika, ya bukaci taron ya nada wasu wakilai su ziyarci kasar Ghana da Afirka ta Kudu da za su rabe tsaki da tsakuwa don gano musabbabin abin da yake tarnake habakar makamashin Nijeriya. Shi kuwa Barista Abubakar tsokaci ya yi kan cewa akwai fa lauje cikin nadi idan aka yi nazarin bambancin ayyukan kamfanonin samar da wuta da kamfanonin rarraba wutar, inda ya yi zargin cewa kamfanonin rarraba wutar babu abin da suke yi illa tara kudi kawai. Ya ce a kasa da shekara biyu kacal, kamfanonin sun kara yawan kudin wuta har sau biyu. Daga nan ya bayar da shawarar a dunkule kamfanonin wuri daya domin a samu sahihiyar ingantacciyar wutar lantarki a Nijeriya. A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kuwa, Moses Mbali mai wakiltar Jihar Adamawa ya yi kira ga gwamnati ne ta karbe lasisin masu rijiyoyin mai don fara hako man gadan-gadan domin habakar tattalin arzikin kasa. Tsohon ministan makamashi da karafa, Alhaji Bashir Dalhatu ya bayyana cewa daya daga cikin matsalolin da suke addabar wutar lantarkin kasar ita ce kin biyan kudin wuta da masu amfani da wutar ke yi. Har ila yau, ya ce akwai kuma bukatar a wayar da kan masu amfani da wuta kan bukatar su rika daidaita yadda suke amfani da ita, a rika kashe kayan lantarkin da ba a amfani da su domin kowa da kowa ya amfana da wutar. Ya kara da cewa, tun da farko da an dora wa kwamitin nauyin bayar da shawara kan yadda za a kawo tsarin shigar da al’umma cikin batun kare kayan lantarki daga barin barnatawa ko sacewa. Dangane da batun tarar da kamfanonin hako mai ke biya, King Alfred Die-Spiff daga Jihar Bayelsa ya bayar da shawarar a rika bayar da wani kaso ga mutanen yankunan da kamfanonin suke aiki saboda su ne na farko da dattin hako man ke shafa.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA