manzon allah yace

Manzon Allah S.A.W yace: "wanda duk yayi salati a gareni ko wacce Juma'a sau arba'in (40) Allah zai shafe zunubansa gaba daya" Manzon Allah S.A.W yace: "mafi kusancin mutane a gareni ranar alkiyama sune wanda suka fi yawaita salati a gareni." Manzon Allah S.A.W yace: " wanda duk ya manta da yin salati a gareni hakika ya kaucewa hanyar Aljanna." Manzon Allah S.A.W yace: "babu wata addua face akwai hijabi tsakaninta da sama har sai an yi salati a gareni, idan akayi salati a gareni sai wannan addua ta keta hijaban nan a dagata zuwa sama." ma'ana duk wata addua da bawa zaiyi bazata wuce sama ba har sai yayi salati ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa salam. Shi yasa yana da kyau idan zamu roki Allah akan bukatun mu, mu fara da salati in mu gama kuma mu rufe da salati. Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu dama duk kasashen musulman da suke cikin tashin hankali. Ameen

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA