saurin fita da anyi sallama

INA MASU SAURIN TASHI DAGA AN IDAR DA SALLAH KAMAR ANA MINTSININSU? TO KU ZO MUJI ABIN DA MANZO (S.A.W) YA FADA. Yau Hadisinmu zai yi magane game da wadanda suke saurin tashi daga sallah da zarar anyi Sallama. Kuma abin haushi sai kaga ma wata kila idan ya tashi ba'abin da ya tsinana. Ko kaga yaje kan gada ya zauna, ko majalisa ko kuma kawai ya tsaya a wajen masallacin sbda bai san tarin ladan da ya bari ba. Daga Abu Huraira (R.A) yace, Manzon Allah (S.A.W) yace, "Sallar mutum a cikin jama'a ana rubanya ladanta a kan sallarsa a gidansa da kasuwarsa, da rubi 25, wannan kuwa sbe idan yayi alwala, ya kyautata a alwala, sannan ya fita zuwa Masallaci,ba abin da ya fito da shi sai Sallah. Babu wani taku da zai yi face sai an daga darajarsa da shi, kuma an kankare masa zunubai da shi, to, idan yayi sallah, MALA'IKUN ALLAH BA ZASU GUSHE BA SUNA YI MASA ADDU'A, MATUKAR DAI YANA WAJEN DA YAI SALLARSA, SUNA CEWA; 'YA ALLAH KA YI MASA RAHAMA, YA ALLAH KAYI MASA GAFARA, YA ALLAH KAJI KANSA'. Ba zai gushe ba a cikin (samun ladan) sallah matukar dai yana sauraren sallah." Wannan Hadisi yana nan a cikin Bukhari (647), da Muslim (649). To 'yan uwana kunji fa wannan falala.To ko limamin garinku ne akace yai maka addu'a zaka ji dadi, balle kuma wadanda basa sabon Ubangijin da ya halicce su. Gaskiya ya kamata mu gyara. Duk masu irin wannan dabi'a nasan zasu karanta. Muna rokon Allah madaukakin Sarki da sunayensa masu tsarki, muna tawasalli da Annabi Muhammad S.A.W, Ya Allah ka yafe mana kurakurenmu, ka sanya albarka a dukkan lamuranmu, ka nisanta mu daga Shaidan datawagarsa, kuma ka kara fahimtar da mu addininka. Ameen

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH