dabiun musulmi na kwarai

DABI'UN MUSULMI NA QWARAI // 10 Da yawanmu mun sani cewa son Annabi ibada ne, don kuwa duk abin da yake imani bai samuwa sai da shi haqiqa ya zama bauta, wannan ya sa wasu in za su roqi mutum wani abu suke cewa don Allah don son Annabi, soyayya gare shi kam kyakkyawar dabi'a ce da kowani musulmi ya zama wajibi ya sifantu da ita, dubi dai abin da Annabi SAW ya ce: لا يؤمن أحدكم حتى أكون أحب إليه من والده وولده والناس أجمعين Dayanku ba ya zama mumini sai ya fi qaunata sama da mahaifinsa da mahaifiyarsa da daukacin mutane. BUKHARI Tunda qaunar Annabi ta zama sharadi na samun imani, haqiqa ta zama dole a duk nau'o'in ibada da mutum zai yi, dubi dai yadda kubutar da iyali ta zama tilas a kan mumini, haka fifita qaunar Annabi ma ta sami wannan matsayin, Annabi SAW ya ce: لا يؤمن عبد حتى أكون أحب إليه من أهله وماله والناس أجمعين. Bawa bai zama mumini sai ya fi qaunata sama da iyalinsa da dukiyarsa da daukacin mutane. MUSLIM kenan ba sauran fakewa da qaunar Annabi wajen yi wa wasu bayin Allah bauta, duk wanda ya rasu ya gama, saura taimakonka yake nema, ba kuma kai ka koma kana neman ya yi maka wata alfarma ba, yi wa Annabi SAW birth day ba ya nuna qauna gare shi, duk mai qaunar Annabi lallai ya miqe ya kama aiki haiqan, shi ya sa Allah SW yake cewa: قل إن كنتم تحبون الله فاتبعوني يحببكم الله ويغفرلكم ذنوبكم والله غفور رحيم. Gaya musu in dai Allah kuke qauna to ku biyo ni Allah zai qaunace ku ya gafarta muku zunubanku, Allah mai gafara ne mai jin wani. A nan biyayya ga Annabi SAW ita take nuna qaunar Allah, ba kide-kide da raye-raye da 'yammata da daddare ba, a dabi'un musulmi na qwarai disco da sunan iyayenmu raini ne da wulaqanci, ya za a nuna qaunar Annabi SAW wanda hakan yake bauta da disco? Da a ce hakan ta fi dacewa da mu lallai da Annabi ya yi umurni da shi tuntuni, kuma lallai da sahabbai da sauran ahlul baiti sun zama na farkon aikatawa, tunda ba su yi ba to ba shakka hakan ta zama mummunar dabi'a. Abin da ba ya boyuwa shi ne, ayannan ta nuna qaunar Allah ne ta wajen kwatanta saqon da Annabi SAW ya zo da shi, to amma yanzu da yawammu mun bar komai mun koma kiran sunan Annabi SAW, wasu kuma sun rabu da Annabin sai dai su kira Aliy RA, wasu su kira Hussain RA, wasu ma sun qare da kiran Abduqadir Jailaniy RL ko Tijjaniy RL ko Kaulahiy da dai sauransu, tabbas wadannan mutane ne, ba a hada bautar Allah da dayansu. Abin da ya rage shi ne biyayya ga Allah sannan Annabinsa, biyayya ga Allah bin umurninsa a Qur'ani da sauran hadisai na qudusi, da duk abin da yake ibada wanda shi ne ya yi umurni amma kai tsaye ko ta hannun manzanninsa, yake cewa a Qur'ani: ومن يطع الله والرسول فأولئك مع الذين أنعم الله عليهم من النبيين والصديقين والشهداء والصالحين وحسن أولئك رفيقا. Wadan da suka yi biyayya ga Allah da manzonsa su ne suke tare da wadan da Allah ya yi wa ni'ima a cikin Annabawa, da siddiqai, da salihan bayi, madalla da wanda yake tare da wadannan. I lallai madalla da wanda yake tare da Annabi a matsayin sahabinsa, madalla da wanda Annabi SAW ya zaba a matsayin sirikinsa, madalla da wanda ya halifanci Annabinsa, madalla da wanda ya yi koyi da umurnin Allah ya qaunanci Annabi da sahabbansa, haqiqa Annabi ya iya zaben sahabbai.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA