ya'mace

CIWON YA'MACE NA YA'MACE NE Wata Amarya ce tayi dare, ta rasa abin hawa, sai can dare sai ga wani Direban babur ɗin Adaidaita sahu (keke Napep), ya taho ɗauke da wata Mata aciki. Amarya ta faɗa masa inda zata. Aka yi sa'a kuwa nan suka nufa. Amarya ta hau babur cikin fargabar, yau wanne irin faɗa Angonta zai yi mata. Don be fi sati biyu da bikin ba, ta tmby zuwa biki, gashi dare yayi mata. Amarya gabanta sai faɗuwa yake, tun tana zancen zuci har ya fito fili. Kira take "yau ban san abinda zan faɗawa Alasan zuciyarsa tayi sanyi ba. Na san dole ransa ya ɓaci. Ba ta ankara ba sai gasu sun ƙaraso inda za ta sauka. Dama gidanta a bakin titi yake. Sai ta ga Ango Alasan a ƙofar gida ya cika ya batse. Amarya ta sauka ta ƙarasa ƙofar gidan jiki a sanyaye. Alasan ya fara cewa cikin faɗa "sai ki koma inda kika fito........" Matar nan ta fito da sauri daga babur ɗin ta nufi Alasan tace "haba Alasan ya zaka faɗi haka? ta nuna Direban babur dama Kawu Mu'azu ne yace mu jira shi, zai kawo mu gida, shi yasa muka yi dare. Sbd kai na ce a fara kawota gida, sannan sai a kaini". Alasan ya saki fuskarsa yace "ai ban sani ba, yi haƙuri. Alasan ya ƙarasa ya durƙusa ya gaishe da ɗan Adaidata sahu. Suka yi sallama suka tafi. Shi kuma Alasan da Amaryarsa suka shiga gida

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA