data
DAGA SAHLU BN SA'AD ASSA'IDY (RA) yace: "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa: "DUK WANDA YA LAMUNCE MIN (YA KIYAYE) ABINDA KE TSAKANIN LEBENSA GUDA BIYU (WATO HARSHE KENAN) DA KUMA ABINDA KE TSAKANIN CINYOYINSQ BIYU (AL'AURA KENAN), NI ZQN LAMUNCE MASA SHIGA ALJANNAH". (Imamul Bukhary ne ya ruwaito hadisin). DARASI : Acikin wannan hadisin Manzon Allah (saww) yana kwadaitar damu muhimmancin kiyaye harshe da kuma al'aura. Domin hakika mafiya yawan laifuffuka ana aikatasu ne ta hanyar amfani da wadannan gabobi guda biyu. Harshe dashi ake aikata shirka, dashi ake yin ridda, dashi ne mutum yake cin naman dan uwansa... Dashi ake mummunar rantsuwa, Kuma adalilinsa akan Kifa mutum acikin wutar Jahannama. Al'aura da ita ake zina, Madigo, Luwadi, Istimna'i da sauran abubuwan da Allah ya haramta.. Ga Azumi nan yana tafe, don haka duk wanda yake son ya samu cikakken ladan azuminsa, to sai ya kiyaye wadannan wurare guda 2. Amatsayinka/Amatsayinki na Daliban wannan zaure mai albarka, Ku rubuto mana kadan daga cikin abinda kuka sani dangane da illolin sakin harshe da kuma Al'aura.
Comments
Post a Comment