tambaya
Mallam don Allah menene hukuncin wanda yayi mafarki da azumi ??? Tambaya ta 2. Menene hukuncin wacce take magana da mijinta ko kuma suka kalle juna bada niyyar sha'awa ba amma kuma sai sha'awar ta motsa har takai da fitar ruwa (maniyyi) ??? Allah ya saka da Alkhairi Mallam (Daga Firdausi Shuaib Gezawa). AMSA ----- AMEEN FIRDAUSI. DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. 1. Wanda yayi mafarki a watan azumi mace ko namiji azuminsa yananan koda kuwa yafitar da maniyyi domin an dauke alqalami akan mutumin da yake bacci harsai ya farka. AMSAR TAMBAYA TA 2. Zataci gaba da azuminta babu komai. Domin Jabir bin Zaid (R.A) yace: "Wanda ya kalli mace ya fitar da maniyyi yaci gaba da azuminsa babu komi a kansa. Wannan shine abinda Imam Shafi'I (Babban almajirin Imam Malik), da Imam Thauri da Auza'iy duk suka tafi akai sunce: Babu wani dalili da yazo cewar fitar da maniyyi kadai yana karya azumi ba tare da jima'I ba. Amma jima'I ko an fitar da maniyyi ko ba'a fitar ba yana karya azumi, kuma akwai kaffara akai. _____________________________________ (Duba sharhin Bukhari ibn Buddal, Juz'ina hudu, shafi na 59). Hakanan wanda ya kalli matarsa har yafitar da maziyyi shima azuminsa yana nan. Amma mazhabar malikiyya suna ganin fitar maniyyi ta hanyar kallo ko runguma yana karya azumi, kuma akwai ramuwa da kaffara akai. Amma maziyyi akwai ramuwa kawai babu kaffara. Domin suna kafa hujja da cewa abinda ake bukata a jima'il shire fitar da maniyyi, saboda haka fitar maniyyi din, daidai yake da jima'I. Saidai sauran manyan malamai sunyi masu raddi cewa: Hukuncin da nassi yazo dashi ya ambaci jima'ine kawai ba fitar da maniyyi ba, kuma suka cigaba da kafa hujjar cewa idan da mutum zaiyi jima'I ba tare daya fitar da maniyyi ba ai zai rama azumine kuma yayi kaffara, kuma da fitar da maniyyi ne, da sai ace mai barci ma idan yayi mafarki yafitar da maniyyi shima yayi kaffara kenan. WALLAHU A'ALAM.
Comments
Post a Comment