brazil

Dan wasan Brazil Dani Albes ya ce ficewar kasar Spain a gasar cin kofin duniya tun a zagayen farko babban darasi ne ga kasashen da ke fafatawa a gasar. A cewar dan wasan na Barcelona samun nasara ba karamin kalubale ba ne. Spain ce ta lashe kofin duniya a kasar Afrika ta Kudu a 2010 kuma a bana tun a tashin farko ne aka yi waje da Spain bayan ta sha kashi a hannun Holland da Chile a rukuninsu na B. “Wannan abin kunya ne”, a cewar Albes tare da yin jaje ga abokan wasan shi na Spain a Barcelona. Wannan dai kamar kira ne Albes ya ke yi wa ‘Yan wasan Brazil don su dage musamman yadda Medico ta rike su babu ci kafin su hadu da Kamaru a ranar Litinin domin samun hurumin tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA