HUKUCIN AMFANI DA ABIN DA YAKE HANA AL'ADA A LOKACIN AZUMI

HUKUCIN AMFANI DA ABIN DA YAKE HANA AL'ADA A LOKACIN AZUMI Tambaya : Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske . Amsa : To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, amma da sharuda guda biyu : 1. Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Al bakarah aya ta 195 2. Ya zama da iznin miji ne, idan hakan ya shafe shi, kamar idan tana iddar da ciyarwa ta wajaba akanshi, sai ta yi amfani da abin da zai hana ta haila don lokacin ya kara tsawo kuma don ta kara masa yawan ciyarwa, to anan bai halatta ta yi amfani da abin da zai hana haila ba saida izninsa, ko kuma idan ya zama maganin zai hana daukar ciki to dole saida iznin miji. Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi sai idan bukatar hakan ta ta so, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye. Duba Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 . Allah ne mafi sani Tambaya : Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske . Amsa : To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, amma da sharuda guda biyu : 1. Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Al bakarah aya ta 195 2. Ya zama da iznin miji ne, idan hakan ya shafe shi, kamar idan tana iddar da ciyarwa ta wajaba akanshi, sai ta yi amfani da abin da zai hana ta haila don lokacin ya kara tsawo kuma don ta kara masa yawan ciyarwa, to anan bai halatta ta yi amfani da abin da zai hana haila ba saida izninsa, ko kuma idan ya zama maganin zai hana daukar ciki to dole saida iznin miji. Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi sai idan bukatar hakan ta ta so, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye. Duba Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 . Allah ne mafi sani

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA