dalilin shan azumi
DALILAN SHAN AZUMI GUDA GOMA SHA BIYU, Sharia ta Amincewa masu larura, su sha azumi, wasu zasu Rama wasu, su ciyar wasu baza, su ramaba, kuma ba zasu ciyar ba, gasu : Na daya: mara lafiya, zai sha azumi, idan ya warke sai ya rama Na biyu: matafiyi, zai sha azumi saboda tafiya, sai ya Rama daga baya. Na uku: mace mai jinin al'ada zata sha azumi idan tayi tsarki, ta Rama Na hudu: mai jinin haihuwa, idan jini ya dauke sai ta rama Na biyar, mai ciki, wacce Taji tsoran, wani Abu zai sameta, ko dan cikin ta Na shida, mai shayarwa ,wacce, Taji tsoran cutuwa, gareta ko dan take, shayarwa. Na bakwai, Tsoho , ko tsohuwa, wadanda, tsufa ya hanasu, azumi, sai su ciyar, Na takwas,: mahaukaci, idan ya warke, sai ya Rama idan kuwa, babu waraka ya sauka akansa babu ramuwa babu ciyarwa Na tara: Yaro, azumi akan yaro ba wajibi bane, sai dan sabawa Na goma, mai farfadiya, idan farfadiya, tazowa mutum, yana azumi, bazai ramaba idan ya farfado Na sha daya,: mai ciwan kishirwa, wanda bazai iya azumi ba,sai ya Dinka ciyarwa Na sha biyu: mai ciwan yinwa, wanda, baya iya daukan lokaci mai tsawo sai yaci abinci, shima sai ya Dinka ciyarwa .
Comments
Post a Comment