maganin ganin annabi (saw)

#MAGANIN_GANIN_ANNABI_(SAWW) Wani mutum yazo wajen SHEHU USMAN 'DAN FODIO (rah) yace masa "Modibbo nazo wajenka ka bani Maganin ganin Annabi (saww) domin kuwa tunda nake ban ta'ba mafarkinsa ba, duk da cewa ina yawaita salati gareshi". Sai Shaikhu 'Dan Fodio yace masa "Idan kaje gida kace ma Matarka ta dafa maka WAKE, ta sanya maka mai Sosai, amma idan ka gama ci, kar kasha ruwa.. Kaje ka kwanta. Duk mafarkin da kayi, kazo ka gaya min, dashi zan hada maka maganin ganin Annabin (saww)". Wannan mutumin ya tafi gida yasa Matarsa ta dafa masa wake, yaci ya Qoshi, har zai sha ruwa, sai ya tuna cewa Shehu yace masa kar yasha ruwa. Don haka sai kawai ya tafi ya kwanta barcinsa. Tunda ya kwanta sai Mafarke-mafarke yake tayi. Amma duk mafarkin nasa bai wuce kan abu guda ba... Wato SHAN RUWA. Sai yayi mafarkin cewa yazo bakin rijiya ko bakin rafi yana shan ruwa mai sanyi. Da ya farka da asuba, yaje yayi sallah sannan ya wuce wajen Shehu 'Dan Fodio domin ya bashi labarin mafarkin da yayi. Sai Shehu yace masa "Dalilin da yasa kayi ta yin mafarkin ruwa, saboda ka kwanta da tsananin tunanin shan ruwan ne azuciyarka. Hakanan idan kana son ganin Manzon Allah (saww) amafarki, dole sai ka zamto cikin Tunaninsa da bin tafarkinsa akoda yaushe (bayan yawan salati da sallama agareshi)". Ya Allah kasa Muyi ta ganin Manzon Allah (saw) aduniya da lahira

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA