tambaya

Assalamu Alaikum Malam. Allah Ya kara maka basira,amen. Meye matata zatayi amfani dashi wadda zai kara mata Ni'ima,saboda idan ina saduwa da ita wani lokaci tana jin zafi sosai idan ya dauke... Daga wani bawan Allah. AMSA **** Yawancin daukewar Ni'ima yana faruwa ne ta dalilai kamar haka: 1. Cututtuka irin wadanda ake dauka alokacin Jima'I (STD). Da kuma cututtukan Mahaifa (disease of the womb). 2. Jinya matsananciya (har irinsu Malaria). 3. Rashin samun isasshen Abinci. 4. Shafar BAQIN ALJANI (Jinnul Ashiq). 5. Rashin kwanciyar hankali atsakanin ma'aurata. 6. Shan magungunan Asibiti (akwai wasu na'ukan maganin asibiti wadanda idan mace tana amfani dasu, to zata samu bushewar farji. Idan ta dalilin STD ne, ko kuma wata Cutar, to dole sai an magance cutar sannan ni'imarta zata dawo. Idan ta dalilin rashin kwanciyar hankali ne ko rashin abinci mai gina jiki, to da zarar an samu chanjin yanayi, to ita ma ni'imarta zata dawo. Idan ta dalilin Shan wasu Kwayoyi ne, to da zarar ta dena sha zata ga chanji. Hakanan za'a iya chanza kalar maganin domin samun daidaituwar ni'imarta. Idan ta dalilin shafar Aljani ne, zaka ga alamomin dhafar aljanu atare da matar. Kamarsu bacin rai, firgita, miyagun mafarkai, Ciwon kai, etc. Kuma Aljanin zai rika zuwa yana saduwa da ita. To dole sai an Qone Aljanin Sannan zata samu lafiya da kuma Ni'ima a farjinta. MAGUNGUNA ************ Ta rika yin matsi da Man Sazabu ko Man Albabunaj, Sannan ta rika yin wanka da dafaffen ruwan da aka dafa da Garin Sazabu ko garin Albabunaj. 2. Ta rika Shan Kunun aya da Kwakwa kullum da yamma. 3. Ta rika shan irinsu Rake da mazarkwaila. 4. Ta rika shan Fruit Salad kullum safe da yamma. 5. Ta rika shan Madara da Zuma. 6.Ta dena yawan tafiya Qafarta ba takalmi.. 7. Ta kula da tsartar Al'aurta ta hanyar tsaftaceshi daga najasa da kuma Aski akai-akai. Allah ya sawwake. Wallahu a'alam.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA