aikin da mai azumi yakamata yayi

MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI DINGA YI (2) ??? Nafil-fili: Anaso mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman kiyamul laili Saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara tabbata a gareshi yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: "Duk wanda yatsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada; an gafarta masa zunubansa da suka gabata". Bukhari ne ya ruwaito shi(1). Haka kuma Manzon Allah (S.A.W) yace: Wanda yayi sallah dare tare da liman har yagama za'a rubuta masa ladan kiyamullaili. Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A) Targib Wattarhib wanda Albani yayiwa tahkiki lambar (1078). "Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana tsawaita karatu a sallar dare a watan Ramadhan fiye da sauran sallolin dare, yace: Manzon Allah (S.A.W) yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a daya, kuma baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikin ta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari. Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A) yazo yana neman izni ayi sallar Asuba. Ahmad ya ruwaito wannan hadisin kuma ya ingantashi. 4. Yawan Zikiri da Salatin Annabi (S.A.W): Abune mai matukar falala mutum ya yawaita Zikiri da Salati ga Shugaban Halitta irin wanda ya tabbata daga bakin Manzon Allah (S.A.W). 5. Ciyar da mai Azumi abin Buda baki: Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum yayi kokari wajen bawa dan uwansa abin Bude baki saboda hadisin da Annabi (S.A. W) yake cewa: "Duk wanda yaciyar da mai Azumi abinda zaiyi bude baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda ya ciyar ba". Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih. 6. Umrah: Yin umrah acikin watan ramadhan ga wanda Allah ya bashi iko yana daga cikin Aiyukan da ake kwadaitar da mai Azumi yayi. Amma duk da haka bai kamata mutum yatafi umrah yabar makwabtansa da danginsa da sauran mabukata a cikin yunwa da halin kakani kayi ba. Kuma ya kamata mu fahimci cewa, ciyarwa itace abinda Annabi (S.A.W) yafi bawa muhimmanci acikin watan Ramadhan. To kunjifa Annabi yake daukar dogon zango idan yana sallar nafila da azumi. Ya Allah kasa muna daga cikin wadanda zaka 'yanta acikin wannan wata, domin darajar Annabi Muhammad (s.a.w). Domin samun darasi irin wannan akoda yaushe.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA