assalam

LITTAFIN UMDATUL-AHKAM Assalamu alaikum warahmatullah, Yan uwa barkanmu da saduwa a wannan littafi mai Albarka, Idan baku mance ba, a darasin da ya gabata, mun tsayane kan bayani gameda hadisi na 65, Cikin BABIN FALALAR SALLAR JAM'I DA KUMA WAJABCINTA: Hadisin da Abdullahi bn Umar yake cewa: Manzon Allah S.A.W yace: (Idan Dayanku matarsa tanemi izininsa don zuwa masallaci, to kada ya hanata). A wata ruwayar kuma Annabi S.A.W yace: (Kada kuhana bayin (mata)Allah daga gidajen Allah). Wannan Hadisi shine wanda kai tsaye ya bawa Mata Yanci da damar zuwa Masallaci suma suyi sallah a ciki, kuma wannan hadisi ya game dukkan mace, daga Yarinya, Budurwa, tsohuwa, Matar Aure, bazawara, kuma bai kawo wani sharadi ba ko qa'ida na yanda matayen zasu kasance, tun daga Fitowarsu daga gidajensu, har zuwa halin da zasu kasance a cikin Masallacin, Hakan Yasa Malaman Fiq'hu suka Kawo Sharudda da Qaa'idoji, Wanda Dolene Mace ta cikasu kafin taje Masallaci, sune kamar haka: 1: Kada ta sanya Turare, ko tayi Kwalliya, akwai hadisin da ya kawo wannan sharadi, inda Annabi ke cewa: (Kuma su fita ba tare da kwalliyaba). A wani hadisin kuma: (Idan dayarku zata masallaci, to kada ta shafa duk wani abin kwallaiya ko Qamshi). Domin wadannan abubuwa (kwalliya da turare) suna ingiza sha'awar namiji, kuma hakan zai zamo silar motsawar sha'awarta itama, kunga qofar barna ta bude kenan. 2. Kada Ta sanya kaya masu Ado, ko masu tsada, ko sanya tufar da zata baiyanar da surar jikinta ko ta baiyanar da kayan da tasanya. 3. Kada su chakudu da Mazaje, ya zamana akwai kebantaccen waje na Mata, tayanda maza bazasu gansu ba, suma bazasu ga mazajenba. 4. Kada suyi magana da kowanne namiji a hanya koda kuwa sun sanshi. 5: Kada su daga sautinsu a yayinda suke tafiya, tayan da mai wucewa zai iya jin sautin muryarsu. Amma babban abin Haushi, a yau, zaka ga Mace wai zata Masallaci, amma ko gidan biki zataje iya kwalliyar da zatayi kenan, gata babu kamun kai inka ganta kai kace sakakkiyar Jaka ce! Surutu kuwa akan titi ko Karnukan anguwar basu fita ba. Kuma Suje Masallaci su fitini masallata, su fitini jama'a sannan su fitini kansu! Yasa, Bayan rasuwar Annabi S.A.W da shekaru kadan, Nana Aisha R.A take cewa: (Inda ace Annabi S.A.W yaga abinda mata suka qirqira daga bayansa, wallahi da ya hanasu zuwa masallaci kamar yanda aka hana Matayen banu Israa'il). To yaya abin yake in ka kwatantashi da Ayau??? Wancanfa Bayan Rasuwar Annabi ne, kuma Nana A'isha nada rai a sannan, kaga ko shekuri 40 baifi ba da rasuwarsa, amma kunga abinda take cewa!!!! Ya abin yake Ayau????? Wal iyaazu billah! Yasa Alal Haqiqah: HANA MATA ZUWA MASALLACI SHINE YAFI ALKAIRI AYAU! DON GUDUN FITINA! Inshallah zanyi rubutu akan wannan maudu'i.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA