harshenka

HARSHENKA ZAKINKA: 1. Harshe wata JAR TSOKA ce wacce Allah yayi maka ita cikin bakinka. Tana da mutukar amfani gareka wajen sanin Dandanon abubuwa da kuma bambancewa tsakaninsu. Bayan wannan Allah ya zuba baiwarsa mai yawa acikin wannan tsokar ta yadda zaka iya Lankwasata ka furta kalmomi tare da taimakon Makogoronka. Harshe shine yake fassara sakon da zuciya take daukr dashi.... Har ma wani lokacin saboda rigima irin na Harshe yakan furta abinda zuciyar ma bata Umurceshi ba. Harshenka kamar wani masifaffen zaki ne mai mutukar Qarfi akulle acikin bakinka, Idan ka barshi akulle, to ka Tsira daga sharrinsa.. Idan ka Sakeshi akan hanyar Alkhairi to kayi sa'a. Amma idan ka sakeshi ya farauci duk abinda yaga dama, to ka hallaka kanka da kanka. Domin kuwa acikin Minti guda zaka iya furta kalmar da zata janyi maka Shekaru dubunnai acikin Wuta. (Allah ya tsaremu). Ya Allah kasa mufi Qarfin Harshenmu da zukatanmu.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA