wani bakabe

Wani Bakabe ne ya kawo wa matarsa cefane babu magi sai ya ce mata: “Ki karbi magi a wurin makwabcinmu mai shago. Koda dare ya yi ya dawo daga aiki sai ya ce a kawo masa abinci, sai aka kawo masa danyen abinci. Ya ce: “Yaya haka?” Sai ta ce: “Ba magi.” Sai ya tashi tsaye ya ce mata: “Bari in je in sayo.” Da ya fita bai dawo ba sai bayan makonni uku. Ya da wo da asuba dauke da magi katon guda. Matar ta ce: “Maigida ina ka shiga?” Ya ce: “Magin ne ya yi wahala.” Can kuma sai ya ce mata: “Ke na manta kayana a mota.” Sai ta rike shi, ta ce: “Ai wallahi kafarka kafata, duk inda za ka.”

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA