zikirin fitowa daga gida

ZAUREN FIQHU ZIKIRIN FITOWA DAGA GIDA ************************** Duk wanda yake bukatar samun Cikakkiyar kariya daga sharrin ALJANU DA MUTANE, tare da kiyayewa da shiriyar Allah acikin dukkan lamarinsa, to aduk lokacin da zai fito daga gidansa zuwa wajen aiki ko kasuwa, ko masallaci, ko balaguro zuwa wani garin, SAI YACE: ''BISMILLAHI TAWAKKALTU ALAL- LAHI. LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL-LAH'' FASSARA: (zan fita) da albarkar sunan Allah, ga Allah na dogara. babu wata dabara ko wani Qarfi sai daga Allah'' Duk wanda ya fadi wannan zikirin Qafa daya yayin fitowarsa daga gida, Mala'ikun Allah zasu ce masa: "AN RIGA AN ISAR MAKA (daga dukkan sharri) kuma an shiryar dakai, kuma an kare ka". Nan take, shaitan zai kauce daga wajensa, sai wani Shaitanin yace ma babban nasu "YAYA ZAKAYI DA MUTUMIN DA AKA RIGA AKA SHIRYAR DASHI, KUMA AKA ISAR MASA, AKA KUMA KARESHI?" (SAHIHUN: Abu Dawud ne ya ruwaitoshi acikin Kitabul Adab, hadisi mai lamba 5,095. Tirmizy ma ya fitar dashi akan lamba ta 3,426. IBNU HIBBAN ya kawoshi acikin juzu'i na 3, shafi na 104. 3 hrs

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA