karya waiyazubillah
KARYA... بِسْمِ اللهِ الْرَّحْمَنِ الْرَّحِيمِ Allah Ta'a Ya ce: "Lallai tsinuwar Allah ta tabbata a bisa MAKARYATA", "Kuma Ya ce: "An tsine wa Makaryata" kuma Ya ce: "Lallai Allah ba ya shiryar da mai barna kuma Makaryaci. A cikin Bukhari ya zo daga ruwayar samurah dan jundub- a cikin Hadisin Annabi (S .A .W)ya ce: "sai muka tarar da wani yana tsaye a kansa da gatarin karfe, sai ya tsaga kansa da idonsa ta kowanne bangare, amma da zarar ya gama sai ya sake komawa yadda yake,Haka zai yi ta yi har zuwa ranar kiyama, sai na ce da su wane ne wannan? sai suka ce" "Wannan shu ne wanda yake fitowa daga gidansa kuma ya yi karyar da kowa sai ya samu labarinta". Manzon Allah (s a w) ya ce: "Mumini yana sabawa da kowacce 'Dabi'a amma ban da yaudara da 'Karya" (Imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi)... lallai wanann hadisin babban wa'azine garemu mu da muke yin FECEBOOK DA SAUREN SOCIAL NETWORK.... gurin yada magana ta Karya mutum 1 zai kirkiri labarin karya ya matsa duka duniya sai taji kuma ta gani... Allah ya shiryemu bisa tafarki madaidaici. RAMADHAN KAREEM.
Comments
Post a Comment