FARILLAN SALLAH Shinfida: Ita sallah ibadace mai matukar mhimmanci da kuma girma a wurin Ubangiji mai girma da daukaka, saboda haka ya zama wajibi akan kowanne mutum daga cikin mu ya kyautata wannan sallah ta hanyar cika farillanta da kuma sunnoninta da mustahabbanta. Farillan Sallah: Idan akace wannan abun farillane to dole ka aikata shi, rashin aikatashi zai janyo matsala a wannan ibadar. Idan ake farillan sallah to anan nufin abubuwa masu matsayi na farko a cikin sallah ta yadda rashin aikata wannan farilla yana zama sanadiyyar rugujewar sallar mutum, kenan ya zama wajibi mu san wadannan farillai da kuma yadda ake aikata su a cikin sallah, domin su ko kabali da ba'adi ba'a yi musu, wadannan farillai sune kamar haka: 1. Niyya: Ana kudurta tane a zuciya ba wai ana furtata da baki bane, abinda ake so adaidai lokacin da zaka yi kabbarar harama zuciyarka ta nufaci sallar da zaka yi. Abinda zai nuna maka ba'a furta lafazin Niyyah kuma furtata bashi da tasiri shine; Idan zaka y...
Comments
Post a Comment