saunawa kagaisar da manzo (saw)
SAU NAWA KA ZAUNA DOMIN GAISAR DA MANZON ALLAH (SAWW) ??? Akwai Ingantaccen Hadisi daga Manzon Allah wanda ya nuna cewa akwai Mala'ika akan Qabarinsa wanda yake isar masa da gaisuwar al'ummarsa gareshi. Sannan kuma duk ranar Juma'ah ana dawo masa da ransa cikin jikinsa, Kuma babu wani wanda zai gaisheshi fache sai ya amsa masa da kansa... Shin ba zaka ji dadi ba, ache ka gaisa da SHUGABAN HALITTUN ALLAH BAKI DAYA?? (SAWW). Ni dai ga tawa gaisuwar nan YA RASULALLAHI.. "Assalamu alaika ayyuhan Nabiyyu wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuhu". Assalatu wassalamu 'alaika ya Rahmatallahi. Assalatu wassalamu 'alaika ya Safwatallahi. Assalatu wassalamu 'alaika ya Habiballahi.. Sallallahu 'alaika wa 'ala aalika wa Sallam.
Comments
Post a Comment