ya da zaa magance fata mai gautsi.
A samu zuma da ‘ya’yan itacen strawberry (za a iya samun wannan ’ya’yan itacen a manyan shaguna). Strawberry na dauke da sinadarin bitamin C. inda zuma take warkar da cututtuka. A daka ‘strawberry’ guda uku, sannan a hada da zuma cokali daya. A shafa a jiki da fuska kullum kafin a yi wanka. Za a wanke bayan minti 15. · Shan shayi mai dauke da ganyen ‘pepper mint’ na taimaka wa jini zaga jiki cikin sauki, shan wannan shayi na wanke maikon da ke makale wadanda suke hana fata sheki. · Za a iya samun lemon tsami da jar albasa ba fara ba. A yanka albasar, sai a markada, sannan a zuba ruwan lemon tsami a cikin markadaddiyar albasa. Daga nan a shafa a jiki da fuska. A jira tsawon minti 10 zuwa 15 kafin a wanke, domin samun sakamako mai gamsarwa. · Idan fata na dauke da bakin kunar rana, sai a rika amfani da mayuka masu dauke da ‘sunscreen’, ko kuma a samu bakar soda (za a iya samun ta a shagunan da ake sayar da kayan yin kek). A zuba cokali kamar 4 na wannan sodar a ruwan dumi. Sai a jika taw...