WANDA YAYI ZINA DA 'YAR UWAR MATARSA

WANDA YAYI ZINA DA 'YAR UWAR MATARSA


ASSALAMU ALAIKUM, Malam Tambaya garemu muke neman a amsa mana. Shin mutum ne shaitan ya rinjayeshi har yayi zina da Kanwar matarsa. Shin aurensa da matarsa yana nan? ko kuwa ta saku automatically tunda har yayi zina da kanwarta?


Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Mun sani dai cewa Allah ya haramta ma muminai Auren 'yan uwa guda biyu alokaci guda. acikin Suratun Nisa'i ayah ta 23 yana cewa: (Kuma na haramta muku) Ku HADA TSAKANIN MATA 'YAN UWAN JUNA GUDA BIYU, SAI DAI ABINDA YA RIGA YA WUCE"

To kunga anan anyi magana ne akan aure. To amma dangane da wannan mas'alar da kuke tambaya akai, Ra'ayin Maluman Musulunci ya rabu gida biyu.

Acikin ALMUGHNEE, ibnu Qudaamah Alhanbaliy (rah) ya kawo ra'ayin Imamu Ahmad bn Hanbal akan wannan mas'alar yace:
"Wanda duk yayi zina da 'Yar uwar matarsa, to ba zai sake Jima'i da matarsa ba, har sai bayan ita wacce yayi zinar da ita ta kammala istibra'i wato Jini uku kenan".

Imamu Ahmad da sauran Malaman da suke kan wannan fahimtar sun dogara ne da wasu hadisai guda biyu wadanda ma'anarsu kusan guda ne. kamar haka:
"DUK WANDA YAYI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA, TO KADA YA ZUBA MANIYYINSA ACIKIN MAHAIFAR MATA BIYU 'YAN UWAN JUNA".


2. "TSINANNE NE DUK WANDA YA ZUBA MANIYYINSA CIKIN MAHAIFAR 'YAN UWA GUDA BIYU"
Alhafiz Ibnu Hajr Al-Asqalaniy (rah) yace wadannan hadisan guda biyu basu da wani asali.


Ibnul Jawzee ya kawo wannan hadisin na biyu acikin wani littafinsa amma bai Jingina masa wani isnadi ba. Hakanan Ibnu Abdil-Hadiy Addamashqee yace : "NA DUBA DUKKAN LITATTAFAN HADISIN NAN GUDA SHIGA INGANTATTU, AMMA BAN SAMU ISNADIN WADANNAN HADISAN BA".

(Aduba Talkheesul Habeer juzu'i na 3 shafi na 343)
Amma ra'ayi mafi daidai shine na Sauran Malamai wadanda suka ce ZINA BATTA LALATA HALATTACCEN AURE. Don haka zinarsa da Qanwar matarsa bai lalata aurensa da matarsa ba.
Sai dai Wajibi ne ita Qanwar tasa taje tayi istibra'i kuma ta tuba ga Allah kafin ta zama halastacciyar matar da wani zai iya aura.
Shi kuwa mutukar laifin ya tabbata akansa, agaban shari'a to haddinsa shine jefewa. Ita kuma idan budurwa ce za'a yi mata bulala 100. idan kuma ta taba yin aure ita ma jefeta za'ayi. Abisa abinda binciken Alkali ya tabbatar karkashin shari'ar addinin islama.


Ya Allah ka kiyayemu daga zina da sauran Kaba'irori. ka kare mana dukkan zuriyarmu. ameeen.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH