KOSAN NAMA

KOSAN NAMA

Shi ma kosan nama kamar kamar kosan dankali yake, sai dai shi da nama ake yin sa.

KAYAN DA ZA KI TANADA

1. Nikakken nama
2. Albasa
3. Attaruhu
4. Kwai
5. Mai
6. Tafarnuwa
7. Garin busashshen biredi (bread crumbs)
8. Gishiri
9. Dunkulen knorr


YADDA ZA KI HADA

Ki sami nikakken nama ki zuba ki zuba masa yankakkiyar albasa da jajjagaggen attaruhu da gishiri da dunkulen knorr ki cakuda, sai ki kawo kwai ki fasa ki kada sannan ki zuba a cikin wannan naman ki juya, ki dandana ki tabbatar komai ya ji. Sai ki sake fasa wani kwan ki kada shi, sai ki ringa tsoma wannan dunkule-dunkulen da kika yi na nama a cikin ruwan kwan, idan kin tsame daga ciki kuma sai ki saka shi a cikin garin bushshen biredi ki jujjuya shi. A gefe daya kuma man ki ya yi zafi a kan wuta sai ki saka ki soya, idan bari daya ya soyu sai ki juya daya barin ma ya soyu. Sai ki tsame shi ki bar shi ya tsane.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH