DUK WANDA YA RIQE MUSULUNCI YA RIQE ADDININ GASKIYA

DUK WANDA YA RIQE MUSULUNCI YA RIQE ADDININ GASKIYA

An taba yin wani Mutum me suna Bayazid Bustami, Masanin addini ne kwarai kuma yana da kokari matuka wajen bautar Allah.

Wata rana yayi nufin wata tafiya sai Wani makwabcinsa Kirista ya nemi su tafi tare, Bayan tafiya me dogon zango sai suka yi zango, lokacin rana ta take.

Bayazid Bustami yace da abokin tafiyarsa ya shiga gari nan kusa da inda sukayi zango ya samu abinci yaci, sai wannan Kirista yace tunda shi Mutumin Allah ne, to ya nemi Taimakon Ubangijinsa Mana ya kawo musu abinci.

Bayazid Bustami ya tashi yayi Sallar Nafila raka'a biyu, sannan ya daga hannu sama ya Roki Ubangiji :
"Yaa Ubangiji wannan bawan naka yana so ya gwada wannan addinin naka, ka kiyaye wannan kyakykyawan sunan na Addininka, ta yadda bazanji kunya agabansa ba cewa wannan addinin naka addinin gaskiyaNe, Ka saukar mana da abinci."
Idar da addu'o'insa keda wuya sai wani mutum ya bayyana gaba garesu dauke da abinci,yayi godiya ga Ubangiji, sukaci abinci suka sha ruwa sannan suka cigaba da tafiya !!
Da yammaci suka sake yin zango, sai Abokin tafiyar Bayazid Bustami (kirista) yace yanzu shi zai shirya musu abincin da zasu ci.

Abun mamaki, bayan addu'o'in wannan kirista, sai Bayazid Bustami yaga wani mutum dauke da kayan abinci ninkin wanda aka kawo musu bayan addu'arsa.
Sai ya tambayi wannan kirista akan wacce irin addu'ah yayi haka.

Abisa mamaki sai wannan kirista yace masa yana so ya fada masa yadda zai Musulunta kafin ya fada masa addu'ar da yayi, nan take Bayazid Bustami ya shiryar dashi yadda zai musulunta.
Bayanda ya karbi musulunci sai ya ce da Bayazid Bustami lalle Musulunci Shine addini na gaskiya acikin addu'ah ta nace :
"Yaa Ubangiji Indai Musulunci Ita ce addinin gaskiya kuma kana jin 'kan bawanka Bayazid Bustami to ka saukar mana da abinci ninkin wanda Bayazid Bustami ya nema Sai kuwa aka karbi addu'ahta".

ALLAHU AKBAR Musulunci Hanyar Rayuwa.
Na samo wannan kissane daga littafin "From Darkness to Light"
wanda Prof. Gazi Ahmed ya rubuta.

Prof. Gazi Ahmed ya bar addinin Hindu ya Musulunta sanadiyyar Mafarkai masu yawa da yayi da Manzon Allah s.a.w.

Yaa Ubangiji Ka Tabbatar damu acikin musulunci!!!

Ka Kashemu acikin Musulunci Ka Kuma hadamu da salihan bayinka a ranar Al-Qiyama.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH