Mijin da ya kamata mata su zaba

Tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta babu mai
shakka akan cewa amfanin zunubi romonsa. Babu
kuma wani mai shakka akan cewa Idan hagu ta kiya,
to ya kamata a koma dama, Kuma kowa ya san cewa
kiwon da ya karbi wani ba shi ne zai karbi wani ba.

Babu wanda bai san amfanin aure shi ne zaman
lafiya ba. Duk auren da aka ce babu zaman lafiya
tsakanin mata da miji, to lallai ba shi da wani
amfani, domin babu wani abu mai amfani da za a
iya samu a cikinsa.

Idan aka ce auren dole a wannan zamani, a tawa
fahimtar ana nufin, aurar da yarinya ga wanda ba
shi ne ta zaba wa kanta ba. Sai mutane suke ganin
wannan a matsayin cin zarafin yarinyar da kuma
rashin wayewa ne. Amma a gaskiyar zance, ni na fi
ganin cin zarafi ga yarinyar da ta nema wa kanta
mijin aure ba tare da mahaifanta ne suka yi ruwa
suka yi tsaki a wajen tantance shi ba, ko ma fito
mata da wanda ya fi dacewa ta aura ba.

Babu laifi mace ta ga tana son wani ba, amma za ka
gano an nade lauje cikin nadi idan ka tambayi
yarinya me ya sa take son saurayin. Sai dai don
kana da cikakken sani akan ka’idar da manzon Allah
(SAW) ya bayar, wadda ya ce a bi ta wajen zaben
miji, za ka sha dariya har sai cikinka ya yi ciwo. Za
ka tabbatar da idan aka bar wannan baiwar Allah da
tunanin kanta a cikin wannan lamari na aure,
karshen lamarin ba zai yi mata kyawu ba da ma shi
kansa mijin.

Abin da Manzon Allah (SAW) ya bayar da shawara
shi ne, a auri namiji mai halaye guda biyu, na farko
mai addini, na biyu kuma kyawun halaye. Ya kuma
tsoratar akan fitina da fasadi mai girma da za su
biyo baya idan ba haka aka yi ba. To yanzu ki
dakatar da karatu daga nan, sai mu yi wata gasa a
tsakanina da ke.

Da ni da ke duk mun yarda da cewar shawarar
ma’aikin Allah ita ce mafificiya, kamar yadda muka
yarda da cewar idan ba a bi maganarsa ba, nadama
za ta biyo baya. To gasar ita ce, mu tambayi
budurwa biyar wadda muka san cewa tana da
wanda take so za ta aura, me ya sa take son ta aure
shi? Idan budurwa uku daga cikin biyar din nan
amsarsu ta dace da shawarar da ma’aikin Allah Ya
bayar, shi ke nan na fadi, idan kuma an samu yin
hannun riga, ni ne mai gaskiya a cikin wannan
zance.

Zamanin dori, lokacin da mahaifa ke zaba wa
’yay’ansu abokan zaman aure, ba a cin karo da
matsalolin aure da muke cin karo da su yanzu,
kamar yawan sakin aure, cin amanar juna, rashin
ganin mutuncin juna, dimbin zargi da dai sauran
matsalolin aure. A fahimtata, mace ta zabo wa kanta
mijin aure ba al’adar malam Bahaushe ba ce ta
asali, daga baya aka kawo mana ita ta hanyar kallon
fina-finan da ke dauke da al’adun wata al’umma
daban. Don haka tun da kiyon bai karbe mu ba, mu
yi hakuri mu bar shi. Mu bar ragamar aurenmu a
hannayen iyayenmu.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH