KOSAN DANKALIN TURAWA KAYAN DA Z A KI TANADA
KOSAN DANKALIN TURAWA
KAYAN DA Z A KI TANADA
1. Dankalin Turawa
2. Nikakken nama
3. Mai
4. Albasa
5. Attaruhu
6. Kwai
7. Tafarnuwa
8. Kori
9. Dunkulen knorr
10. Gishiri
YADDA ZA KI HADA
Ki sami dankalin turawanki dai-dai yawan da kike so ki yi, ki feraye shi ki wanke, sai ki zuba ruwa a cikin tukunya ki zuba wannan dankalin a ciki har sai ya dahu. A gefe daya kuma kin tanadi nikakken namanki, kina iya sayen nikakken namanki daga shagunan da ake sayar da kayan masarufi. Sai ki kawo dankali ki marmasa shi da hannu sosai, ki kawo nikakken namanki ki zuba akai, da gishiri da kori da jajjagagen attaruhu da albasa da dunkulen knorr da tafarnuwa idan kina so ‘yar kadan. Sai ki juya su gaba daya su juyu sosai. Sai ki dunkula su kamar kwallo dai-dai girman da ki ke bukata. Idan kin gama sai ki bar shi ya sha iska kamar minti biyar. Ki fasa kwai ka da ki zuba komai a ciki, ki kada shi sai ki ringa tsoma wannan curin da kika yi na kwallon dankali cikin ruwan kwan, ki juya shi sosai ki tabbata kwan ya shiga jikin dankalin sosai. Kina yi kina sakawa a cikin mai mai zafi domin suya, idan gefe daya ya soyu sai ki juya daya gefen shi ma ya soyu.
Comments
Post a Comment