Mahimmancin Sakin fuska ALLAHU AKBAR!!!

Mahimmancin Sakin fuska ALLAHU
AKBAR!!!

Wata rana sahabban manzon
ALLAH (S.W.A) sun kawo qarar SAYYIDINA
ABUBAKAR WUrin Manzon Allah (s.w.a)
suna Cewa Ya Manzon Allah: Abubakar ya
kasance idan munka hadu dashi yana rigan
bamu hannunsa muyi musabiha cikin farin
ciki da sakin fuska, Amma ynzu idan muka
hadu dashi se ya sunkuyar da kanshi qasa
se mun fara bashi hannunmu sannan ze
miqo nasa. Se manzon Allah yace aje Maza
akira Abubakar cikin lokaci se gashi yazo
yana zuwa se (s.a.w) yace kaji abunda
sahabbaina sunka fada Gaskia ne. Se
Asyyidina Abubakar cikin girma mawa ya ce
ya wanda bakinsa baya qarya, Eh hakane
gaskia ne suka fada Amma ina da hujja se
yace jiya nayi mafarkin wani katafaren gda
wanda babu abunda ke cikinsa se kayan
alfarma da more rayuwa da jin dadi wani
abunma hankali da tunani baya misaltasu
Allah (S.W.A) ya fadamin cewa: babu
wanda ze shiga gdan face Wanda idan ya
hadu da mutane yana rigan miqa masu
hannu a gaisa kuma cikin sakin fuska da
murmushi, to shine nike masu kwadayin
wannan gda da su shigeshi shi yasa na bari
su rinqa fara miqo min hannunsu suna
farin ciki da sakin fuska da murmushi.
Allahu Akbar! Idan Muka lura muka natsu
yan uwa zamu fahimci abunda hadisin
nannan ke nufi zamu ga akwai fala me
dunbin yawa aciki da kuma wa'azantarwa
akan fara miqawa dan uwanka hannu kana
me fari'a da sakin fuska tare da murmushi
ida kuka hadu. Allah Yasa Mu dace Dunia
Da LahiraM Don Allah Dan Uwa Kada Ka
Karanta Kabarshi kai kadai Ka Turawa Yan
Uwanka Musulmai Masoya Manzon Allah
(S.w.a) kasamu ladan tuna tarwa su kuma
su qaru da abunda ka tura masu.

Comments

Popular posts from this blog

FARILLAN SALLAH

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH