Matakan magance kawayen da suke kashe aure
Babu shakka dole ne kowane mutum ya zama yana
da mutanen da ya amincewa da su a rayuwa. Kamar
yadda ango yake da abokai haka ma matar take da
kawaye, wadanda ta amince da su, amma wani
lokaci irin wadannan kawaye ne ke cin amanar
ma’auratan har ta kai sun kashe musu aure.
Wasu daga cikin kawayen amarya da abokan ango
sun san abin da suke yi, kuma soyayyar da suke
nuna wa ango da amarya ta Allah da Annabi ce,
amma wasu babu abin da suka kudurce a zuciyarsu
sai bakin-ciki da tsurku da tsugudidi. Wasu ma
kawayen daga bisani amarya take gamuwa da su
bayan ta tare a gidanta, inda masu kananan shekaru
da ’yan mata masu zuwa hira da kallon fina-finai da
matan aure makwabta da masu sayar da kayayyaki
iri-iri da kuma dattijai da tsofaffi masu zuwa hira
tare da yin gulmace-gulmace.
Idan aka yi rashin sa’a aka samu amarya ba mai
nisan tunani ba ce, sai irin wadannan kawaye su
fara kawo mata maganganu iri-iri. Har wani lokaci
su rika gaya mata cewa ai sun ga mijinta da wance
ko kuma sun gan shi a wuri kaza. Ita kuma daga nan
sai ta hau kan abin da aka fada mata ba tare da ta yi
bincike ba, ta rika fushi tana zare idanu tana cika
tana batsewa. Shi kuwa angon ya rasa laifin da ya yi
mata. Ta haka shi ma idan ba mai nisan tunani ba
ne sai ya yi zuciya, shi ma ya rika yin fushi, ya rika
daure mata fuska. Daga nan sai alaka ta lalace a
fara kai kashedi wurin iyaye da waliyyan da suka
daura auren.
Idan kuwa aka yi sa’a amaryar ko angon masu zurfin
tunani ne za ka ga irin wadannan miyagun kawaye
ba za su ci nasara a kan su ba, saboda sun san duk
gutsuri-tsomar da suka kawo musu ba za su yarda
da ita ba, balantana ma su amince da gulmace-
gulmacen da ake yadawa a tsakaninsu.
Amaren da suke da kulaficin kawaye, wadanda duk
wacce suka gani sai su yi kawance da ita su jawo ta
jika ba tare da tantancewa ba, su ne suka fi fadawa
cikin wannan tarko don ba kasafai namiji ya fiye yin
abota mai zurfi ba kamar mace. Su mata suna da
saurin yarda da amince wa juna. Irin amaren da
suke tara kawaye a gidajensu babu shakka suna
cikin hadarin fadawa tarkon gulma da yamadidi,
kuma idan ba su yi hattara ba alakarsu da
mazajensu na cikin hadari.
Akwai wacce da ta tara kawayenta sai ka ji ta saki
baki ta kwashe duk abin da ya gudana tsakaninta da
mijinta ta fada musu, su kuma su yi ta dariya. Wasu
da suke jin haushin ta a cikinsu sai su kuma su
kwashe su gaya wa mijin ko ’yan uwansa, daga nan
sai a fara rikici. Wasu kawayen kuwa sai su yi amfani
da abin da suka ji daga amaryar su yi kulle-kullen
da za su yi su hada alaka da mijinta su ja hankalinsa
ta dabara su yi ta yi mata sharri har ya sake ta su
kuma su aure shi.
Wasu kawayen ma irin matan nan ne da suka kashe
auransu sai su dawo su tare a gidajen amare su yi ta
kulle-kulle har sai sun ga sun kashe wa duk amaryar
da suka hadu da ita aure. Za ka ji suna yi wa
amaren karyar cewa auren dole aka yi musu ba
kaunar mazan da suka aura suke yi ba, ko ka ji suna
gaya mata cewa sai ta tashi tsaye idan ba haka ba
uwar mijinta da ’yan uwansa za su hana ta jin dadin
aure. Kuma su ce mata sai ta tashi tsaye ta nemi
maganin da za ta mallake mijinta. Daga nan sai su
sanya ta a hanyar bin bokaye da ’yan bori.

Comments
Post a Comment