Wata rana sayyidina Ali R.A yake bada labarin cewa farko-farkon aiko annabi s.a.w wani lokaci yaje masallacin ka'aba

Wata rana sayyidina Ali R.A yake bada labarin cewa farko-farkon aiko annabi s.a.w wani lokaci yaje masallacin ka'aba


Yana sallah kawai saiga manyan kafiran kuraishawa sunzo,
wannan ya turoshi,wannan ya jawoshi ya dungureshe,


Haka sukaita cin mutuncin annabi s.a.w,
Sayyidina Ali R.A yace mukuma a lokaci muna kanana bamu isa mu tabuka komai ba,


Saiga sayyidina Abubakar R.A ya taho a guje, yana zuwa ya fara mangare kafiran nan ya samu wannan doke ya ture wancan, yana fadin "yanzu ashe zaku iya kashe mutumin da yace ku kadaita Allah"


Sayyidina Ali R.A yace a haka dai suka hakura suka bar annabi s.a.w.
Allahu akbar


Allah ya kara mana san annabi da iyalan gidansa da sahabbansa matsarkaka.
Ameen

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH