wani labari mai cike da mamaki
Wata rana wani dan sarki yana wasa a kofar fada
sai wani
bakin maciji ya lallabo ya cije shi, yaro ya yi kara
ya fadi yana
shure-shure kafin ka ce me har ya ce ga garinku.
Hankalin sarki
da fadawa ya tashi, sarki ya baza dogarai su nemo
macijin nan
su kashe shi, maciji kuwa ya shige cikin gari yana
ta gudu
fadawa na binsa har ya gaji sun kusa kama shi,
sai ya zo ya
tadda wani masaki yana saka ya ce masa "ka ji
kaina ka ceci
rayuwata ka boye ni kar fadawan sarki su kashe
ni" sai masaki
ya ce "ni ba ni da wajen boye ka", sai maciji ya ce
"ka bude
bakin ka in shiga idan sun wuce sai in fito na
rantse maka ba
zan cutar da kai ba", sai masaki ya bude bakinsa
maciji ya
shige, bayan fadawa sun wuce sai masaki ya ce
"to fito sun
wuce", maciji ya ce "in fito? ina! ai ni na samu
wajen zama, na
huta da yawo sai in yi ta cin hanjinka da hantarka
su ne
abincina". Masaki yai juyin duniya amma maciji ya
ki fita, ya yi
ta yawo ya na kuka, kwana da kwanaki duk ya
rame ya
kanjame. Rannan ya na yawo sai ya gamu da
tsuntsu sai
tsuntsu ya ce "kai kuwa kukan me ka ke yi?" sai
masaki ya
kwashe labari kaf ya fada masa sai ya ce "ba don
halin 'yan
Adam na butulci ba, da na taimake ka", sai masaki
ya ce haba!
Ya za ka taimake ni, in yi maka butulci ai ba na yi
haka ba" sai
ya ce "to ka je ka kwanta a rana ka daga bakinka
kamar ka
mutu", sai masaki ya ce "to" ya je ya kwanta ya
daga bakinsa,
can! Maciji ya ji zafi ya yi yawa sai ya fiddo
kanshi ya sha iska
sai tsuntsu ya yi farat ya jawo shi suka kashe shi.
Masaki ya ce "na gode" sai tsuntsu ya ce "to
yanzu ka samu
kaji biyu ka dafa ka ci shi ne maganin raunin da
yai maka a
ciki". Ko da masaki yaji haka sai yayi farat ya
kama tsuntsu ya
ce "dama ina kiwon kaza sai in gama da kai in
yanka". Tsuntsu
ya yi ta kuka amma masaki ya tafi dashi gida ya
kife da kwando
ya na can ya na wasa wuka sai matarsa ta zo
wurin tsuntsu ta
ce "ya aka yi mijina ya kama ka?" Tsuntsu ya
kwashe labarin
yadda suka yi da masaki ya gaya mata sai ta ce
"gaskiya ya yi
maka butulci bai kyauta ba amma kar ka damu
bari in bude ka
ka tafi in yazo sai in ce bansan yadda aka yi ka
gudu ba" sai
tsunstu ya ce "da kin kyauta kuwa", sai ta bude
kwando tsuntsu
kuwa kawai sai ya kwakwule idonta daya ya tashi
abinsa ta yi
ta ihu tana kuka.
A CIKINSU WA YAFI BUTULCI???

Comments
Post a Comment