ya da zaa magance fata mai gautsi.

A samu zuma da ‘ya’yan itacen strawberry (za
a iya samun wannan ’ya’yan itacen a manyan
shaguna). Strawberry na dauke da sinadarin bitamin
C. inda zuma take warkar da cututtuka. A daka
‘strawberry’ guda uku, sannan a hada da zuma
cokali daya. A shafa a jiki da fuska kullum kafin a yi
wanka. Za a wanke bayan minti 15.
· Shan shayi mai dauke da ganyen ‘pepper mint’
na taimaka wa jini zaga jiki cikin sauki, shan wannan
shayi na wanke maikon da ke makale wadanda suke
hana fata sheki.
· Za a iya samun lemon tsami da jar albasa ba
fara ba. A yanka albasar, sai a markada, sannan a
zuba ruwan lemon tsami a cikin markadaddiyar
albasa. Daga nan a shafa a jiki da fuska. A jira
tsawon minti 10 zuwa 15 kafin a wanke, domin
samun sakamako mai gamsarwa.
· Idan fata na dauke da bakin kunar rana, sai a
rika amfani da mayuka masu dauke da ‘sunscreen’,
ko kuma a samu bakar soda (za a iya samun ta a
shagunan da ake sayar da kayan yin kek). A zuba
cokali kamar 4 na wannan sodar a ruwan dumi. Sai
a jika tawul a rika tsomawa ana shafawa a wurin da
ya yi baki.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH