BLACKBERRY KASHI NA BIYU

Ranar dai na fito fili na fada masa abin dana keso take ko yamin Alkawari washe gari zai siya min, har ma cewa yayi zai zo ya dauke ni
muje shago in zabi irin duk wacce nake so, ai ranar tsabar murna ko abinci na kasa ci haka nazauna na fada duniyar tunanin yadda rayuwa zata kasance tayi dadi in na samu BlackBerry ina zaune ni daya ina dariya wannan daren dai ko bacci ban iya nayi na kwana tunanin BlackBerry....


Tun da sassafe na gama aikin gida da wanda aka sani da wanda ba'a sani ba dan kawai in birge umma ta barni in fita, dan kuwa na mata karyan zani gaida kawata hajara bata da lafiya da yamma.


Ta ji dadin ayyukan da na mata, dan haka ina fada mata ko musu batayi min ba tace a dawo lfy Allah kare nace Amin.


Karfe hudu na sameshi a bakin titi cikin motarsa ya bude min ko musu banyi ba na shiga da murna ta, ina Allah-Allah mu isa shago, ko gaisawa ba muyi ba na soma tambayar sa ta ina shagon yake, yamin murmushi yace dani karki damu yanzu zamu isa.


Kofar wani katon gida naga ya tsaya, na kallesa na ce nan ne shagon? Ya ce min a'a nan gidan cin Abinci, ya dago min wata karamar jakar takarda
mai ruwan kasa a jiki naga ansa
BlackBerry, tuni murna ta cika ni nace Ashe har ka siya, yace eh...muje in munci abinci munyi hira sai in baki na mai dake gida, da sauri na fito na bishi ina ganin yau burina zai cika.


tafiya muke har ya kaini cikin wani falo da'alama gida ne daga nin falon kasan ba kirar kamarin mai kudi bane ko tallaka hmmm ba shi duk abinda ake bukata akwai a falon kaf wani abin burgewa sai ka leka dakin dake cin sanan kaga wani makeken gado mai kyau da isa hmmmmm sai dai kagani kawai...........


wato Abinda da ya kasance shine...


Mu hadu a kashi na uku

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH